Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa al’ummar Jihar Imo alkawarin taimaka musu wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihar.
Kazalika, Shugaba Buhari ya kuma yi alkawarin warware matsalar ababen more rayuwa a fadin jihar.
Ya yi wannan alkawari ne yayin wata ziyara ta musamman da ya kai jihar Imo ranar Alhamis, duk da barazanar da ’yan a-waren Biyara suka yi na kai masa farmaki.
Da yake jawabi yayin bude titin Egbeada zuwa Onitsha da aka kammala a Owerri, Buhari ya yaba da irin cigaban da jihar ke samu.
A cewarsa, babu wata al’umma da za ta samu samu ci gaba matukar tana fuskantar barazanar tsaro, amma ya yaba da irin namijin kokari da Gwamna Hope Uzodinma ke yi a jihar.
Shugaba Buhari, ya ce “Na zagaya kuma na ga abubuwan da suka burge ni.
“Babu wata al’umma da za ta cigaba in har babu tsaro da ababen more rayuwa, amma sai ga shi abun ba haka yake a nan ba.
“Zan yi amfani da karfin da kundin tsarin mulki ya ba ni wajen taimaka wa gwamnan jihar nan.”
Uzodinma, a yayin jawabinsa, ya roki shugaban kasa, da ya taimaki jihar wajen kawo karshen matsalar tsaro musamman a Owerri da ma jihar baki daya.