Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya sha alwashin hanzarta kera makaman nukiliya tare da sanya su cikin shirin fara amfani da su nan take.
Da yake magana a wajen faretin bikin
cika shekara 90 da kafa rundunar sojin kasar, Mista Kim ya yi gargadin shafe duk wata kasa da ta nemi sa-zare da
Pyongyang a kan wannan aniya.
- Malamin Addini ya bijire wa Sarkin Musulmi, ya gudanar da Sallar Idi a Sakkwato
- Fiye da mutum 3,000 sun mutu a teku yayin shiga Turai a 2021—UN
Wakiliyar BBC ta ce hotunan da kafafen watsa labaran kasar suka wallafa sun nuna babban makami mai-linzami na kasar samfurin Hwasong-17 wanda aka kammala gwajinsa a watan jiya, bayan tabbatar da cewa zai iya kai wa kasar Amurka.
Wasu hotunan tauraron dan Adam na baya-bayan nan sun nuna cewa ana ci gaba da aikin dawo da ramukan kera makaman da aka lalata a shekarar 2017 bayan Kim Jong-un ya tattauna da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump.