Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin jihar na shirin kafa dokar haramta yawon kiwo a jihar.
Masari ya jaddada sukarsa ga yawon kiwo da cewa ba Musulunci ba ne, don haka ya kamata makiyaya su tsaya a guri guda su kiwata dabbobinsu.
Gwamnatin Jihar Katsina, a cewarsa, “Tana so ta kafa dokar haramta yawon kiwo, amma kafin mu yi hakan za mu samar da wuraren da dabbobin za su yi kiwo.
“Ya kamata makiyaya su tsaya a wuri guda. Ya kamata a kyamaci yawon kiwo domin a ganinmu yawon kiwo ba Musulunci ba ne.
“Me ma zai sa mutum ya tara dabbobin da ba zai iya ciyarwa ba, su rika shiga gonakin mutane, ya ce hakan daidai ne ? Gaskiya hakan bai dace ba.”
A hirar da shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin din Channles ya yi da shi, Masari ya ce Gwamantin Tarayya ta riga ta ba da kasonta na kudade a kokarinta na taimaka wa gwamnatin jihar domin kaddamar da shirin samar da gandun kiwo.
“Mun riga mun fara, Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira bililyan N6.2, mu kuma a matsayin gwamnatin jiha za mu ba da Naira biliyan 6.2. Manufar ita ce ganin Fulani sun zauna a wuri daya sun daina yawon kiwo.”
Tuni dai gwamnatocin jihohin da ke yankin Kudancin Najeriya suka kafa dokar haramta yawon kiwo a fadin yankin.
Wasu daga cikin jihohin sun riga sun rattaba hannu a kan dokar da Kungiyar Gwamnonin Kudu ta ba wa wa’adin ranar 1 ga Satumba, 2021, wasunsu kuma ba su yi hakan ba tukuna.