✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan iya sadaukar da rayuwata ga Katrina – Ranbir Kapoor

Masu magana kan ce ranar wanka ba a boyen jibi, hakan ne ya sa soyayya tsakanin jaruman fina-finan Indiya Ranbir Kapoor da Katrina Kaif da…

Ranbir Kapoor da Katrina KaifMasu magana kan ce ranar wanka ba a boyen jibi, hakan ne ya sa soyayya tsakanin jaruman fina-finan Indiya Ranbir Kapoor da Katrina Kaif da suka dade suna boyewa ta fito fili, inda jarumin ya ce zai iya sadaukar da rayuwarsa ga Katrina don dorewar farin cikinta.
Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta TOI a makon da ya gabata.
Ya ce: “Akwai mutane da zan iya sadaukar da rayuwata saboda dorewar tasu, wadannan kuwa su ne iyalina, wadanda suka hada da Ayan da Katrina; wadda take da babban matsayi a zuciyata da Rohit Dhawan; abokina da muka girma tare, sai Aisha Dibetri; abokiyata a makaranta da kuma Imtiaz Ali da Anurag Basu kasancewar sun taka muhimmiyar rawa a rayuwata.”
Idan ba za a manta ba dai jaruman sun dade suna boye soyayyar da ke tsakaninsu, inda suka rika karyata batun soyayyar, sai dai a kwanakin baya aka samu bullar hotunan jaruman suna hutawa a wata kasa. A yanzu dai jarumin ya daina karyata batun soyayyar da ke tsakaninsa da  Katrina.