✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan dora daga inda El-Rufai ya tsaya a Kaduna —Uba Sani

Uba Sani ya ce kafa ’yan sandan jihohi da bai wa masarautu ’yancin cin ganshin kansu ne mafita daga mastalar tsaro

Dan takarar gwamnan Kaduna a Jam’iyyar APC, Uba Sani, ya ce kafa ’yan sandan jihohi da bai wa masarautu ’yancin cin ganshin kansu ne kadai mafita daga matsalar tsaro.

Uba Sani wanda shi ne Sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya yi alkawarin dorawa a kan ayyukan gwamnan jihar mai ci, Nasir El-Rufai.

Dan takarar ya ce ya yi damarar yin kabakin aiki musamman a bangaren ilimi, lafiya, harkar noma, matasa da kuma bunkasa sana’o’in mata.

Ya bayyana haka ne a ganawarsa da ’yan kasuwa, mata, matasa, manoma, shugabannin addinai, kungiyoyi da sauransu a lokacin taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a Kafanchan, Karamar Hukumar Jema’a ta jihar.

A cewarsa, kowa yana sane da yadda El-Rufai ya sauya fasalin jihar cikin shekara takwas, don haka yake da aniyar dora ire-irensu don inganta jihar.

Ya bayyana cewa gogewar da ya samu a majalisa ce ta ba shi damar yin takarar gwamnan jihar.

A nata jawabin, mataimakiyar dan takarar, Dokta Hadiza Balarabe, cewa ta yi zabar APC ba da tabbacin ci gaba da yin ayyukan alheri ne.

Ta ce manufar taron shi ne jin ta bakin daidakun mutane kai tsaye don sanin yadda za a magamce musu damuwa.