✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan dora a kan kyawawan manufofin Buhari idan aka zabe ni – Tinubu

Ya ce ba zai yi watsi da manufofin gwamnatin APC ba

Dan takarar Shugaban Kasa na jam‘iyyar (APC) Bola Ahmad Tinubu, ya ce idan har ’yan Najeriya suka zabe shi, zai dora a kan kyawawan manufofi da shirye-shiryen da Shugaba Muhammadu Buhari ya faro.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin yakin neman zabensa da aka gudanar a Owerri da ke jihar Imo.

Ya ce manufofin Buharin ne sanadiyyar farfadowar tattalin arzikin Najeriya, wanda PDP ta durkusar tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki.

Tinubu ya kuma ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai habaka fannin ilimi da tsare-tsaren kasa da kuma alkinta ma’adanai.

“Za mu ci gaba da dora shirye-shiryen ci gaba da APC ta fara, don ba za mu yi watsi da su ba,” in ji shi.

Yayin da Shugaba Buhari yake mika masa tutar jam’iyyar, dan takarar godiya ya yi ga dafifin da al’ummar jihar suka yi don tarbarsu, inda ya yi alkawarin ba zai ba su kunya ba idan suka zabe shi a 2023.

%d bloggers like this: