Sanata Datti Baba-Ahmed, tsohon sanata mai wakiltar shiyya ta daya, kuma dan takarar shugabancin kasa ya ce tsaf zai doke Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Datti Baba-Ahmed wanda shi me shugaban jami’ar Baze da ke Abuja wanda kwanan nan ya bayyana aniyarsa na neman zama shugaban kasa, ya ce yana da duk abin da ake bukata domin doke Buhari a zaben mai zuwa.
“Ina yi wa Buhari maraba domin tsayawa takarar 2019. Ba zai ji da dadi ba. Kada ka manta sau uku Buhari yana tsayawa takara amma bai samun nasara, sai lokacin da PDP ta yi wasu kura-kurai da ya sa ‘ya’yanta suka fice suka koma APC, sannan suka taimaka masa ya lashe zabe,” inji shi.