✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan daina amfani da kafafen sada zumunta —Thierry Henry

Henry ya dauki matakin ne, don yaki da wariyar launin fata da ake nuna wa bakaken 'yan kwallon kafa a duniya.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Barcelona da kasar Faransa, Thierry Henry, ya ce zai daina amfani da kafafen sada zumunta har sai mahukunta sun dauki mataki kan yadda ake ciki zarafin bakaken fata.

Tsohon dan wasan, wanda yanzu yake horar da kungiyar kwallon kafa ta CF Montréal da ke kasar Faransa, ya dauki mataki ne don kwato wa bakaken fata ’yanci.

“Barka dai jama’a, daga gobe (Asabar) da safe zan daina amfani da shafukan sada zumunta har sai mahukunta sun dauki mataki kan yadda ake nuna wa bakaken fata wariyar launin fata a kafafen sada zumunta.

“Nuna wariyar launin fata, cin zarafi da sauransu sun yi yawa, don haka tilas a dauki mataki.

“Har sai an duba wannan bukata tawa, sannan zan sake bude kafafen sada zumunta, ina fatan hakan ba zai dauki lokaci ba”, cewar Henry.

’Yan wasan kwallon kafa suna fuskantar kalubale, musamman a hannu fararen fata a lokuta da dama, idan ana buga wasanni.

Ana yawan kiran bakaken fata da birai ko kuma wata dabbar da ke nuna kaskanci a gare su.

Wannan dalili ne ya sa Henry daukar wannan hukunci don yaki da irin wannan dabi’a daga fararen fata.

Ba shi ne karon farko faruwar irin haka ba ke nan, ko a ranar 3 ga watan Janairun 2013, dan wasan AC Milan, Kevin-Prince Boateng, ya fuskanci irin wannan cin kashi daga ’yan kallo.

Hakan ta sa dan wasan cire rigarsa tare da ficewa daga fili, daga bisani ragowar ’yan wasan suka goya masa baya, suka cire rigunansu sannan suka fice daga filin wasa, suna allawadai da dabi’ar ’yan kallon.

%d bloggers like this: