Tonto Dikeh, ’yar wasan fim din Nollywood kuma mataimakiyar dan takarar Gwaman Jihar Ribas a Jam’iyyar ADC a zaben 2023, Tonte Ibraye, ta ce za ta dade tana nadamar rashin taimaka wa wani mara lafiya.
Tonto Dikeh ta bayyana takaicinta bisa yadda ta yi watsi da rokon da wata mata ta yi mata na ta taimake ta da kudi domin kula da lafiyar danta, wanda daga baya ya rasu.
- Salman Rushie Zai Iya Rasa Idonsa Bayan Harin Da Aka Kai Masa
- DAGA LARABA: Kayan mata: Gyaran jiki ko janyo cuta?
Dikeh, ta bayyana hakan a shafinta na Instagram, inda ta bayyana dalilin rashin taimaka wa mahaifiyar rayon da ke cikin damuwa.
Ta ce ta ki tababar bayar da taimakon ne saboda zargin masu damfara ta intanet ne suka turo sakon, saboda kwanaki kadan kafin nan an damfare ta ta intanet.
Tonto Dikeh ta ce, “A makonnin baya na taimaka wa wata mai goyon bayana da kusan rabin Naira miliyan (N370,000), wadda ke cikin matsala kuma tana shayarwa.
“Bayan mako guda na so in ji halin da suke ciki. Amma kash! Sai na samu an rufe shafin Instagram din da ta turo min sako. Na dauke shi a matsayin kaddara.
“Na ji haushi sosai kuma na yi tunanin an yi amfani da ni an cuce ni, amma na ci gaba da harkokina.
“Ba a dade ba, kwana biyu da suka gabata, aka sake turo min sakon neman taimakon kudin sayen magani; Nan take na goge sakon.
“Washegari da bude sakonni da aka aka turo min, sai na ga sakon mahaifiyar yaron tana shaida min cewa dan nata ya rasu.
“Gaskiya na yi kuka sosai, har sai da idona ya rika min zafi; Zuciyata ta kadu matuka,” inji jarumar.
Ta kara yin bayanin cewa, za ta dade tana nadamar abin da ya faru kuma, “Zan dade ina tsanar kaina.
“Dubi girman asarar da aka yi a sanadiyyar karya da yaudarar da wani mutum daya ya yi… Ina mika ta’aziyya ga mahaifiyar yaron da duk wanda lamarin ya shafa!!”