✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan ci gaba da kokarin kwatowa ‘yan Najeriya ‘yanci- Atiku

Dan takarar zaben shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 23 ga Fabrairu 2019 Atiku Abubakar, ya ce zai ci gaba da kwatowa ‘yan Najeriya…

Dan takarar zaben shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 23 ga Fabrairu 2019 Atiku Abubakar, ya ce zai ci gaba da kwatowa ‘yan Najeriya ‘yancin su don tabbatar da sun samu romon dimokuradiyya a kasar duk da watsi da karar da suka shigar gaban Kotun Kolin Najeriya yau Laraba ta yi.

A wata sanarwa da Mai bawa Atiku shawara a kan watsa labarai Mista Paul Ibe, ya fitar na cewa, sanarwar da Kotun kolin ta yi na yin watsi da karar, ba zai rage masa karfin gwiwa ba.

Atiku, ya kara da cewa, wannan hukuncin kotun na daya daga cikin kalubalen dimokuradiyyar Najeriya, yanzu ya ragewa ‘yan Najeriya su yi alkalanci ko Kotun Kolin ta yi adalci?