Dauda Kahutu Rarara ya yi alkawarin ci gaba da daukar nauyin ’yan sandan nan uku da Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta kora daga aiki bisa zargin harba bindiga sama a lokacin da suke rakiyar mawakin a kauyensu.
Mawakin ya sha alwashin ci gaba da biyansu albashin da ake ba su wata-wata da kuma sauke sauran nauyin da ke kansu na yau da kullum a cewar jaridar Manhaja.
- An yi wa kananan yara 2 yankan rago a Filato
- Adamawa: Sanarwar ‘nasarar Binani’ daidai ne —Kwamishinan Zabe
’Yan sandan uku — Sufeto Dahiru Shu’aibu da Abdullahi Badamasi da kuma Isah Danladi masu mukaman Sajan — sun shiga cikin matsala ce bayan da suka yi harbi a iska da bindigarsu ta aiki a cikin jama’a lokacin rakiyar mawakin aka dauka a bidiyo, aka watsa a dandalin sada zumunta na Intanet.
Bayan da rundunar ta janye jami’an daga rakiyar mawakin tare da kai su hedikwatarta a Abuja, Rarara ya yi kokarin samar musu sassauci, amma hakan bai yiwu ba.
A cewar mawakin, “Na tuntubi mutane daban-daban don su shiga maganar tun kafin a kore su, amma duk da shiga tsakani da kuma rokon da na yi, amma rundunar ta dage kan korarsu.
“Don haka bayan sun sanar da ni, sai na tambaye su nawa ne albashinsu, sai suka gaya mini, ni kuma na yi masu alkawari cewa, daga yanzu, zan ci gaba da biyansu albashin da rundunar ke biyan su,” in ji Rarara.
Mawakin ya ce, ’yan sandan da aka kora sun daukaka kara kan hukuncin, idan sun yi nasara za a iya mayar da su bakin aiki, idan kuma a karshe hakan bai yiwu ba, zai ci gaba da biyansu albashin.
Rundunar ’Yan sandan ta Kasa ta ce ta kori jami’an ne a wani mataki na ladabtarwa, bayan wani bincike da ta gudanar kan harbin da ake zarginsu da yi, ta kuma same su da laifin da ta kira na harbi ba bisa ka’ida ba da barnatar da harsashi da kuma rashin sanin makamar aiki.
Mawakin ya samo ’yan sandan ne daga rundunarsu ta Kano bisa wani tsari da aka fito da shi na bayar da su aro ga mai bukata a matsayin ’yan rakiya bayan biyan wasu kudi na ka’ida.
Rarara ya are su ne a bisa wannan tsari, a inda suka raka shi kauyensu Kahutu da ke Jihar Katsina wacce ke fama da matsalar tsaro.