✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan bunkasa kasuwar Dawanau- Inji Sabon Shugabanta

Sabon shugaban kungiyar ci gaban kasuwar kayan abinci ta Dawanau (DMDA) Alhaji Mustapha Yusif Mai Kalwa, ya ce zai shugabanci kasuwar bisa gaskiya da adalci…

Sabon shugaban kungiyar ci gaban kasuwar kayan abinci ta Dawanau (DMDA) Alhaji Mustapha Yusif Mai Kalwa, ya ce zai shugabanci kasuwar bisa gaskiya da adalci tare da tabbatar da ganin kasuwar ta kara bunkasa ta yadda za ta dace da zamani.
Sabon shugaban ya yi wa daukacin ‘yan kasuwar da masu hada-hada a cikinta albishirin nan gaba kadan kasuwar za ta zama abar misali, musamman ma ganin tana daya daga cikin manyan kasuwannin kayan abinci ta duniya.
Ya ci gaba da cewa a tsawon wa’adin shugabancinsa na shekaru hudu, zai ba da himma ne don samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci.
“Za mu yi kokarin samar da titin mota a cikin kasuwar da filin ajiye motoci don kiyaye cinkoso. Ina da burin gina magudanan ruwa da yin ciko a bangaren kasuwar da ke zaizayewa da kuma kakkafa fitilu a ciki da wajen kasuwar.” Inji shi.
Shugaban ya yi kira ga ‘yan kasuwan kan mahimmancin biyan haraji, kuma ya sanar da cewa za su kara inganta tsaro da gyara cibiyar sadarwar kasuwar, domin samar da sahihan bayanai na farashin kayayyaki. Daga bisani ya nanata muhimmancin hadin a tsakanin ‘yan kasuwa. “Ya kamata ‘yan kasuwa su rika warware matsalolinsu ta hanyar yin sulhu.”
A karshe ya yaba wa gwamnatin Jihar Kano a kan kokarin da take yi wajen inganta yanayin harkokin kasuwanci a Jihar. “Ya kamata gwamnatin tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) su tallafa wa ‘yan kasuwar Dawanau.” Inji shi.