✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan bar Kaduna gaba daya idan na kammala wa’adin mulkina a 2023 — El-Rufa’i

Ya ce ba yana son yin katsa-landan ga magajinsa

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi alkawarin barin Jihar kwata-kwata ranar 29 ga watan Mayun 2023 bayan mika mulki ga magajinsa saboda ya guji yi masa katsa-landan.

Ya kuma nuna fatansa cewa dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ne zai gaje shi, kodayake ya ce shi ma sam ba zai saka masa baki a sha’anin mulki ba.

El-Rufa’i, wanda ya yi jawabi yayin wani taro da aka shirya na mazabar Kaduna ta Tsakiya ranar Litinin, ya ce ya san Uba Sani sama da shekara 20, kuma ya nuna halaccinsa a siyasance.

Gwamnan ya kuma shawarci mutanen Jihar da kada su dame shi da kamun kafa a wajen neman mukamai a wajen dan takarar idan ya lashe zabe.

Shi ma a nasa jawabin, Sanata Uba Sani ya ce shi dalibi ne a makarantar siyasar El-Rufa’i sama da shekara 20 kuma ya sami ‘digiri’ iri-iri a cikinta.

Dan takarar, wanda kuma shi ne Sanata mai ci da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, ya yi alkawarin dorawa a kan manufofi da ayyukan El-Rufa’i idan aka zabe shi.

Ya kuma ce gwamnati ita kadai ba za ta iya daukar ragamar harkar ilimi ba, dole sai daidaikun masu hannu da shuni sun shigo sun bayar da gudummawarsu.