Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya bukaci al’ummomin Jihar da su fito su kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Matawalle ya ce wajibi ne a kafa rundunar matasa majiya karfi da za su rika murkushe hare-haren ’yan bindiga a kauyuka da garuruwa.
“Ya kamata al’ummomi su zama masu lura da zakulo baragurbin da ke cikinsu domin kar a yi kitso da kwarkwata.
“Akwai masu jin dadin hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa, amma duk wanda ya tabbata ba shi da hannu a ciki, shi ma ya fito ya rantse da Allah kamar yadda nake yi,” inji shi.
Gwamnan na Zamfara ya yi kiran ne a ranar Juma’a, a lokacin gudanar da addu’o’i na musamman kan cikarsa shekara biyu a kan mulki.
Ya ce gwamnonin Arewa sun yi ittifaki kan yadda kowace jiha za ta kafa rundunar matasa da za su rika mara wa jami’an tsaro baya wajen dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran bata-gari a jihohin.
Ya ce gwamnonin za su fito da hanyoyin da sarakunan gargajiya zu tantance su kuma zabo matasan da za su kasance a cikin rundunar da za ta rika kare al’ummomi daga mahara.
“Kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar nan shi ne abin da ya fi min komai muhimmanci, zan kuma ci gaba da bin halastattun hanyoyi wajen samar da tsaro da aminci mai dorewa a cikin al’ummomi.”