✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zamfara: ’Yan bindiga sun kashe mutum 4 a Talata Mafara

’Yan bindigar sun kashe mutum hudu sun jikkata wasu da dama a Zamfara

Mahara da ba a san ko su wane ne ba sun bindige mutum hudu tare da jikkata wasu da dama a Jihar Zamfara.

’Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 11 na safiyar Asabar, suna harbin mazauna unguwar Garagin Jidda da ke Karamar Hukumar Talata Mafara.

Mazaunan sun shaida wa Aminiya cewa ce za a binne mamatan a makabartar Mayanchi saboda gudun kar ’yan bindigar su kai farmkai a lokacin jana’izar.

Zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton, wakilin Aminiya bai samu kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ba domin jin ta bakinsa.