✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta yabi yadda Buhari ya tunkari ‘yan bindiga a Zamfara

Jam’iyyar PDP ta samu rabuwar kai game da yadda Gwamnatin Tarayya take tunkarar hare-hare da sauran matsalolin tsaro a jihar Zamfara. Sakataren PDP reshen jihar…

Jam’iyyar PDP ta samu rabuwar kai game da yadda Gwamnatin Tarayya take tunkarar hare-hare da sauran matsalolin tsaro a jihar Zamfara.

Sakataren PDP reshen jihar Zamfara Hashimu Modomowa, ya ce matakan da gwamnatin Shugaba Buhari ta dauka sun taimaka sosai wurin magance matsalolin tsaro a jihar.

Sanarwar ta Modomowa ta ci karo da zargin da tun farko Kwamishinan Raya Karkara na Jihar Abubakar Abdullahi ya yi, inda ya ce gwamnatin ba ta damu da matsalar tsaron da ke addabar jihar ba.

Kwamishinan ya zargi Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da karkata zuwa ga cutar coronavirus fiye da yakar ‘yan bindigar da ke addabar Zamfara.

Sai dai jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta nesanta kanta da kalaman nasa wadanda ta ce na iya kawo sabani tsakanin jihar da gwamantin tarayya.

Sakataren jam’iyyar ya ce gwamnatin tarayya ta yi rawar gani wurin magance matsalar tsaro a jihar.

Matakan, “Sun hada da kafa rundunonin sojin kasa da na sojin sama a jihar karkashin rundunar Operation Hadarin Daji,” a cewarsa.

Modomowa ya yaba da yadda gwamnatin ta amince da hakar ma’adanai a jihar, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi da rage aikata laifuka a jihar.

Zamfarawa a cewarsa na godiya saboda matakan da gwamnatin tarayya ke dauka domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.