Mahaddatan Al-Kur’ani daga Jihohin Zamfara da Kano sun dauki kambin Gasar Musabakar Al-Kur’ani ta Kasa karo na 35 da aka kammala a Kano.
Gwarzon Shekarar na gaba daya a musabakar shi ne Muhammad Auwal Gusau daga Jihar Zamfara, wanda ya doke sauran abokan karawarsa a rukunin haddar Izu 60 da Tajwidi da Tafsiri.
- Yadda aka kama wata mata da ke shayar da maciji nononta
- Mahaifin dalibar da aka sace a kwalejin Kaduna ya rasu
- Dalilin da Buhari ya gaza cika alkawuransa –Bashir Tofa
Bayan bayyana shi, an nada masa rawani a matsayin gangaran, mahaddacin Al-Kur’an na kololuwa, bisa al’adar musabakar.
Mahaddaciyar da ta zama Gwarzuwar Shekara, a bangaren mata na Izu 60 ita ce Nusaiba Shuaibu Ahmad daga Jihar Kano.
Maddatan Al-Kur’ani fiye 300 ne suka fafata a tsakaninsu a tsawon mako guda a musabakar wadda kuma aka kammala a ranar Asabar, 27 ga Maris, 2021.
Kwamitin Alkalai mai mutum bakwai ne ya rika bin kwakkwafi a yayin da kowanne daga cikin mahaddatan yake karatu a bisa mum bari.
Ayyukan alkalan sun hada ta jan baki, bibiyar yadda mahaddaci ke cika ka’idojin Tajwidi a yayin karatu, karfin hadda, nutsuwa da sauransu.
Kowanne bangare an ware masa alkali mai sa ido tare da ba da maki a kansa daga cikin alkalai shida da ke aiki a lokaci guda yayin da daya ke zaman jiran ko-ta-kwana.
Rukuni shida da ne aka fafata a musabakar da suka hada da Izu 60 ta Tajwidi da Tafsiri, Izu 60 da Tawjidi, Izu 40, Izu 20, Izu 10 sai kuma Izu biyu.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Babban Limamin Masallacin Kasa, Farfesa Shehu Ahmad Sa’id Galadanci, manyan malamai, alarammomi, da sarakakuna da dama sun halarci taron rufewar.
Musabakar da ta samu wakilici daga jihohin Najeriya ta kuma samu halarcin mutane daga sassan Najeriya.