’Yan bindiga da dama sun sheka lahira a wani dauki-ba-dadi da aka yi tsakaninsu da jami’an tsaro a Jihar Zamfara.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta hannun kakakinta, SP Muhammad Shehu, ta ce jami’an tsaron sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga kusan 200 da suka tare hanyar Gusau zuwa Sakkwato.
“Rundunar ’Yan Sandan Zamfara ta yi nasarar dakile harin gungun wasu ’yan bindiga a kan hanyar Gusau zuwa Sakkwato, kusa da Dogon Karfe a Karamar Hukumar Bakura.
“Maharan sun yi kokarin tare hanyar domin yi wa matafiya fashi, amma jami’an tsaron da ke kan hanyar sun dakile yunkurin nasu.
“A dauki ba dadin da aka yi da ’yan bindigar na awa daya, da yawa daga cikinsu sun samu rauni, amma sun kwashe gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe saboda yawan adadinsu da ya kai 200.
“Yanzu haka an bude titin bayan dauki-ba-dadi da aka yi da su, kuma ababen hawa sun fara wucewa, an kuma yi wa dajin da ake tsammanin ’yan bindigar na ciki kawanya,” inji Shehu.
Sai dai ya ce jami’an tsaro biyar, ciki har da ’yan sanda hudu sun rasu yayin artabu da ’yan bindiga a garin Gora Namaye a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar.