✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman Mutum (3)

Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi. Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai…

Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi. Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi kokari ka samu amintacce daya daga cikinsu, ba za ka samu ba. ’Ya’yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa’a. Sarkin da yake yin shari’a ta gaskiya da ganin mugunta ya san ta. Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa? Allah Yana kin masu ma’aunin algushi. Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta. Ubangiji Ya ba mu ido don mu gani, Ya ba mu kunne don mu ji. Idan barci ne sana’arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka samu wadataccen abinci. Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fariya a kan ya iya ciniki. In ka san abin da kake fada, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu’ulu’ai tamani. Sai wawa kadai yake daukar lamunin biyan basussukan da bako ya ci, ya kamata a karbi dukiyarsa jingina. Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji dadinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba dade zai zama kamar yashi cike da bakinka. Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaki ba tare da shiri ba. Mai baza jita-jita ba ya da sirri, ka yi nesa da mai yawan surutu. Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu. Dukiyar da aka same ta ba wahala, amfaninta kadan ne.

Kada ka daukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji Shi zai yi sakamako. Ubangiji Yana kin wadanda suke awo da ma’aunin algushi. Ubangiji Ya kayyade hanyoyinmu, ta kaka wani zai ce ya fahimci rai? Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa’adi za ka mika wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da-na-sani nan gaba. Sarki mai hikima zai bincika ya gane wadanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi. Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya boye maSa ba. Sarki zai zauna dafa’an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci da adalci da daidaita. Karfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce. Wani lokaci sai mun sha wuya muke sake hanyoyinmu.

Ubangiji ne Yake mallakar tunanin sarki a sawwake kamar yadda Yake yi da ruwan rafi. Ko da a ce dukan abin da kake yi daidai ne, ka tuna fa Ubangiji Ya san manufarka. Ubangiji Ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka mika maSa hadayoyi. Girman kai da fariya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne. Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka samu abin da zai ishe ka ba. Dukiyar da aka tara ta hanyar rashin gaskiya takan kare nan da nan, takan kuma kai ga mutuwa. Mugaye, tasu ta kare saboda muguntarsu, gama sun ki yin abin da yake daidai. Mutane masu laifi sukan bi ta karkatacciyar hanya, marasa laifi kuwa suna aikata abin da yake daidai. Gara zama a sako da zama a gida daya tare da mace mai mita. Mugaye sun zaku su aikata mugunta, ba su yi wa kowa jinkai. Sa’ar da aka hukunta mai girman kai, ko marar tunani yakan koyi wani abu, mutum mai hikima yakan koyi abin da ake koya masa. Adali ya san tunanin mugaye, yakan kuwa zama sanadin lalacewarsu. Idan ka ki jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba. Kyauta a asirce takan kwantar da zuciyar wanda yake fushi da kai. Sa’ar da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi bakin ciki. Mutuwa tana jiran wanda ya ki bin hanyar hankali. Sa kai cikin nishadi, wato shan ruwan inabi da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba. Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu. Gara ka zauna a hamada, da ka zauna tare da mace mai mita, mai yawan kai kara. Mutane masu hikima suna zaune da wadata da nishadi, amma wawaye da zarar sun samu kudi sukan kashe su nan da nan. Ka yi alheri ka yi aminci, za ka yi tsawon rai wadansu kuma za su girmama ka, su yi maka abin da yake daidai. Sarkin yaki mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke takama da shi. Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake fada. Ba kalmar da ta fi “Fadin rai” dacewa ga mutum mai girman kai, mai fariya marar tunani. Malalacin mutumin da ya ki yin aiki, kansa yake kashewa.

Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta kaka yakan bayar da hannu sake. Ubangiji Yana kin hadayar da mugaye suka mika maSa, tun ba wadda suka mika ta da mugun nufi ba. Ba a gaskata shaidar makaryaci, amma mutumin da yakan yi tunani a kan al’amura, akan karbi tasa. Adali ya tabbatar da kansa, haka ma mugun mutum yakan yi da’awa, cewa shi ma ya tabbatar da kansa. Hikima da hazikanci da basira, ba komai suke ba gaba da Ubangiji. Kana iya shirya dawaki don zuwa yaki, amma nasara ta Ubangiji ce.

Karin Magana 20:5-30,20