✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zalunci: An fitar da sunayen ’yan sandan da za a hukunta

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas ta fitar da jerin sunayen ’yan sandan da za ta hukunta bisa laifukan cin zarafi da karya hakkin dan Adam…

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas ta fitar da jerin sunayen ’yan sandan da za ta hukunta bisa laifukan cin zarafi da karya hakkin dan Adam a jihar.

Jerin sunayen na dauke da sunan ’yan sandan da nau’in laifukan da suka aikata da kuma matakin binciken da ake yi a kan su.

Wannan yana dauke ne cikin wata takarda da Atoni-Janar na jihar, Moyosore Onigbanjo (SAN) ya fitar a ranar juma’a.

Ya ba da tabbacin dukkanin ’yan sandan za su fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata.

Shi ma gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “yau babbar rana ce a Jihar Legas da za mu kawo karshen zaluncin ’yan sanda.

“Kamar yadda muka dauki alkawarin hukunta duk wanda aka kama da laifin cin zarafi ko danne hakkin dan Adam, to ga jerin sunayen ’yan sandan da aka samu da laifukan cin zarafi da danne hakkin dan Adam a jihar Legas”.