Bayan shekara biyu da harin bata-tari a lokacin zanga-zangar EnsSARS, Kamfanin Retail Supermarket Nigeria Limited (RSN), ya sake bude reshensa na Shoprite da ke Lekki a Jihar Legas.,
Tun bayan harin da bata-garin suka sace kayan Shoprite da sunan ganima a lokacin zanga-zangar a watan Oktoban 2020 wurin yake a rufe.
- Buhari zai saya wa NDLEA da fadar shugaban kasa motocin N23bn
- An kwaso ’yan Najeriya 542 da suka makale a Dubai
Da yake jawabi yayin sake bude shagon, shugaban kamfanin RSN, Hubertus Rick ya ce, “Shekaru biyu da suka gabata mun dauki mataki mai wahalar gaske na rufe Shoprite saboda matsalar tsaro.
“Mun yi haka ne saboda kare lafiyar kwastomominmu da ma ma’aikatanmu saboda muhimmancin da muke bai wa rai.
“A yau muna farin cikin sanar da sake bude shagon don ci gaba da harkokinmu,” in ji shi.
A yayin zanga-zangar da ta rikide ta koma tarzoma, bata-gari sun yi amfani da damar wajen fasa shaguna da kwashe dukiyar jama’a.
Tarzomar ta lakume rayuka da dama baya ga kone-kone da masu boren suka yi ta yi, musamman a Jihar Legas, da wasu yankuna na kudu maso Yammacin Najeriya.
Yankin Lekki ya dauki hankalin duniya matuka a yayin tarzomar, inda masu zanga-zangar suka yi cikar kwari kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.
Yadda sojoji suka fatattake su ya jawo ce-ce-ku-ce da zargin kisan gilla, har aka kare da kafa kwamitin bincike.
Sojoji da wasu masu binciken kwakwaf dai sun karyata bidiyon da aka yada cewa sojoji sun yi amfani da karfi fiye da kima wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zangar.
An yi zanga-zangar EndSARS ne domin kin jinin sashen ’yan sanda na musamman mai yaki da ayyukan fashi, wada ya sanya masu damfara da intanet a gaba.
Matasa sun yawaita zargin jami’an rundunar, wadda aka rusa daga baya, da tsare mutane ba bisa ka’ida ba, zalunci, kisan gilla da kuma karya doka.
Daga bisani dai Shugaba Buhari ya rusa rundunar tare bayar da umarnin gudanar da bincike.
Ya kuma yi alkawarin yin sauye-sauye a aikin dan sanda ciki har da karin albashi da bayar da horo ga jami’an rundunar.