Ambaliyar da ta biyo bayan mamakon ruwan sama ta yi awon gaba da wani mutum bayan ya kammala kwashe iyalansa daga gidansa a jihar Legas.
Mutumin na daga cikin mutum biyu da ambaliyar ruwa ta kashe bayan mamakon ruwan sama da aka yi a safiyar Litinin.
- HOTUNA: An raba wa ’yan kasuwar Kantin kwari tallafin Atiku na N50m
- Mahaifin da ya yi wa ’yarsa mai shekara 17 fyade ya nemi afuwa
Ya koma gidansa da ke Iyana Ipaja bayan ya yi nasarar dauke matarsa da ’ya’yansa hudu domin karbar wasu takardu a lokacin da ruwan ya yi gaba da shi.
Lamarin dai ya faru ne a yankin Iyana Ipaja da kuma yankin Command da ke jihar ta Legas.
Mahaifin ’ya’ya hudun da aka bayyana sunansa da Alfa, an yi zargin cewa, ruwan ya yi awon gaba da shi ne sakamakon ambaliyar da ta mamaye mafi yawan yankunan aramar hukumar Alimosho ta jihar.
Wasu daga cikin titunan da abin ya shafa sun hada da na Ajayi da Olubodun Ifesowapo da Olubodun da Fafunwa da Ipaja ta Yamma da Toluwani da ke karamar hukumar ta Alimosho.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, Ibrahim Farinloye, ya ce mamacin ya yi yunkurin tserewa ne tare da matarsa da ’ya’yansa hudu.
Farinloye ya ce, abin takaici ya faru ne lokacin da marigayin ya koma gidansa da nufin ya dauko wasu kayayyaki da suke amfani da su.
“Amma an kai masa dauki da wasu mutane biyu tare da taimakon al’umma.
“An kwashe dangin Alfa zuwa gidan danginsa.
“Wani matashi kuma ya fada cikin ruwa bayan gadar katako ta balle a Unguwar Command. Ruwan ya tafi da shi kafin taimakon ya kai gare shi,” inji Kakakin na NEMA.