✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi

Gwamnatin ta ce za ta ci gaba da aiki da sauran hukumomi domin daƙile iftila'in ambaliyar ruwa a jihar.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun fara raba kayayyakin tallafi ga mutum 507 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar a 2024.

An gudanar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a a Ƙananan Hukumomin Kibiya da Madobi, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa kayayyakin ga waɗanda suka ci gajiyar shirin.

Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ne, ya wakilci gwamnan.

Gwamnan, ya gode wa NEMA bisa goyon bayan da ta ke bai wa jihar, tare da yaba wa SEMA saboda jajircewarta wajen tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda abin ya shafa.

“Muna da niyyar ci gaba da aiki tare da hukumomin da suka dace don inganta shirye-shiryen daƙile iftila’i a Kano,” in ji shi.

“Gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa don kare lafiyar jama’a.”

Daraktar Janar na NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta ce wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na taimaka wa waɗanda ambaliya ta shafa.

Ta hannun Kwamandan NEMA a Kano, Dokta Nura Abdullahi, ta bayyana cewa an amince da tallafin ne bayan Gwamnatin Tarayya ta karɓi rahoto kan ɓarnar da ambaliyar ta haifar.

“Gwamnatin Tarayya tana jajanta musu kan yanayin da suka shiga,” in ji ta.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhu 500 na shinkafa mai nauyin kilo 25, buhu 500 na masara mai nauyin kilo 25, katan 45 na tumatirin gwangwani, katan 45 na man girki, katan 45 na maggi, da buhu 20 na gishiri.

Sakataren Zartarwa na SEMA, Alhaji Isyaku Kubarachi, ya buƙaci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya dace.

Wani daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Nura Sani, ya nuna jin dadinsa.

“Wannan tallafi zai taimaka mana sosai a wannan mawuyacin lokaci. Muna godiya ga gwamnati bisa ƙoƙarinta,” in ji shi.