’Yan sanda sun yi nasarar kashe wani shugaban ’yan fashi, Fidelis Ekata, a wata musayar wuta a yankin Uromi na Jihar Edo.
Kafin mutuwarsa, Fidelis Ekata ya kasance jagoran wata kungiyar asiri kuma yana daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Benin a lokacin zanga-zangar #EndSARS ta 2020, wanda jami’an tsaro ke neman sa ruwa a jallo a kai.
- NAJERIYA A YAU: Wahalar Fetur A Najeriya: Da Sauran Rina A Kaba
- Medinat Abdulazeez Malefakis: Gwanar yaki da ta’addanci
Kakakin ’yan sandan jihar, Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da mutuwar Ekata, ya ce ya mutu ne a sakamakon raunin harbi da ya samu a musayar wuta da ’yan sanda.
Ya bayyana cewa ’yan sanda sun samu rahoto cewa an ga shugaban ’yan fashin da jima ana nema ruwa a jallo a yankin Uromi.
Ba tare da bata lokaci ba rundunar ta aike da jami’anta zuwa yankin, inda ganin su ke da wuya sai ’yan fashin suka bude musu wuta, daga nan aka yi ta dauki-ba-dadi a tsakaninsu har ta ’yan sanda suka harbe shi.
Kontongs ya ce an garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Uromi don duba shi, amma likitoci suka tabbatar da rai ya riga ya yi halinsa.
Ya kara da cewa rundunar na gudanar da bincike domin cafke ragowar ’yan fashin da suka tsere da raunukan harbi a yayin gumurzun.