✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakzaky: ’Yadda ’yan sanda suka tarwatsa zaman dirshan din ’yan Shi’a a Abuja

A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan Shi’a magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky suka sake mamaye wasu manyan tituna a Abuja a wata sabuwar…

A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan Shi’a magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky suka sake mamaye wasu manyan tituna a Abuja a wata sabuwar zanga-zangar neman a sako shugabansu da gwamnati ke tsare da shi tun shekarar 2015 da kuma wakilansu 115 da aka kama a ranar Litinin din da ta wuce.

Tun cikin shekarar 2017 magoya bayan Sheikh Zakzaky suke gudanar da zanga-zanga a Abuja tare da yin zaman dirshan a Unity Fountain domin tursasa wa gwamnati ta saki shugabansu.

Zanga-zangar ta ranar Talata, magoya Zakzaky sun taru ne a yankin Mabushi sannan suka biyo hanyar da ta bi mahadar Berger inda suka nufi Kasuwar Wuse, kuma shaidu sun ce, zanga-zangar tana neman komawa hargitsi a kusa da kasuwar ne sai jami’an tsaro suka hanzarta rufe kofofin shiga kasuwar, sannan ’yan sanda suka yi amfani da borkonon tsohuwa tare da watsa musu ruwa don tarwatsa su.

Wasu majiyoyi sun ce an ga manyan motocin jami’an tsaro sun killace dandalin Unity Fountain wanda hakan ne ake ji ya sanya ‘’yan Shi’ar tattaruwa a Mabushi, inda suka shirya yin tattaki zuwa hedkwatar Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa da ke Maitama, Abuja.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Kwamishinan ’Yan sandan Birnin Tarayya, Abuja, Abubakar Bello ya bayar da umarnin hana ci gaba da zanga-zangar ’yan Shi’ar a birnin bayan sun yi wani gangami a dandalin Unity Fountain, inda suke zaman dirshan don neman a sako Zakzaky.

Kuma a ranar Litinin ne ’yan sanda suka yi amfani da karfi wurin tarwatsa ’yan Shi’a da ke zanga-zanga a dandalin Unity Fountain da ke Abuja, kiuma wadanda suka shaida lamarin sun ce ’yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wurin korar masu gangamin. 

’Yan sanda sun kama karin ’yan Shi’a a kan 115

Kakakin ’yan sandan Abuja, Anjuguri Manzah ya ce an kama karin magoya bayan Zakzaky da suka sake yin zanga-zanga a ranar Talata a Abuja. Ya ce, sun samu bayanan da suka nuna dubban ’yan Shi’a sun hallara a Kasuwar Wuse, inda suka hana sauran jama’a hanyar shiga cikinta, kuma ’yan sanda suna zuwa, sai ’yan Shi’ar suka shiga jifarsu da duwatsu da sauran abubuwan masu hadari. Ya ce bayan wani lokaci ’yan sandan sun samu nasarar shawo kan lamarin tare da kama wadansu daga cikinsu.   

A ranar Litinin ’yan sandan sun kama ’yan Shi’a 115 a lokacin da suka yi zanga-zangar da ta jawo arangama da ’yan sanda. ’Yan sandan sun kuma ce masu zanga-zangar sun lalata motocin jami’an tsaro tare da ji wa ’yan sanda 22 rauni. Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta kuma gargadi mabiya Shi’ar su daina tsare hanya a zanga-zangar tasu. Kuma ta ce za ta gurfanar da mutanen da ta kama a gaban kotu bayan ta kammala bincike.

R undunar ’Yan sandan Abuja, ta ce ta samu kayayyaki kamar su gwafa da rodi da duwatsu da kuma jajayen kyallayen da ake daurawa a ka.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a wasu shafukan sada zumunta sun nuna ’yan Shi’a mabiya Zakzaky suna jifar motar ’yan sanda wacce ita kuma ta rika watsa musu ruwa.

Sakataren Harkokin Ilimi na Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Zakzaky, Malam Abdullahi Musa ya ce sun kai wadansu mambobinsu wasu wurare masu zaman kansu don yi musu jinya. “Mun zo don mu ci gaba da zanga-zangarmu ta neman a sako shugabanmu Sheikh Zakzaky, amma kamar yadda Kwamishinan ’Yan sanda ya yi alkawari, sai muka iske an killace dandalin Unity Fountain da ’yan sanda sama da 200 da sojoji ke tallafa musu. Mun yi musu magana muka bukaci su bar mu mu ci gaba da zaman dirshan din da muke yi, saboda muna da ’yancin hakan, amma suka ki. Don haka take muka rubuta takardar koke muka tunkari Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa don kai korafinmu. Sai jami’an tsaron suka kaddamar da hari a kanmu suka yi amfani da borkonon tsohuwa da ruwa don tarwatsa mu. Mun turje musu ta jifarsu da duwatsu, amma sai suka bude wuta ga wadansu mambobinmu suka kashe wasu suka raunata da dama. Sun tafi da gawarwakin wadansu mambobinmu, sun zauna ma a kan wasu suka tafi da su inda ba mu sani ba.”

Babu wanda aka kashe – Kwamishinan ’Yan sanda

Sai dai Kwamishinan ’Yan sandan Birnin Tarayya, Abubakar Bello ya shaida wa wata kafar labarai ta tarho cewa babu wanda aka kashe a yayin zanga-zangar, kuma ya tabbatar da kama mutum 115 da suka hada da ’yan daba da masu tausaya wa ’yan Shi’a da ’yan tashin hankali na kungiyar IMN, a lokcin fafatawa da ’yan sandan da suke kokarin hana su tayar da zaune-tsaye a Abuja.

Babu sojoji a cikin lamarin – Hedkwatar Tsaro 

Hedkwatar Tsaro ta ce ba a tsoma sojoji a cikin tarwatsa ’yan Shi’a masu zanga-zangar ba. Sai sai Rundunar Sojin Najeriya ta ki cewa uffan kan zargin sanya hannun sojoji a lamarin.

Kakakin Hedkwatar Tsaro Birgediya Janar John Agim, ya shaiwa wa wata kafar labarai ta tarho cewa sabanin rahotannin da ake samu a wasu kafafe, ba a tsoma sojoji a cikin lamarin ba. Ya ce magance irin wannan matsala aiki ne na ’yan sanda ba sojoji ba.

A gudanar da bincike kan hautsinin – PDP  

Jam’iyyar PDP mai adawa ta bukaci a hanzarta gudanar da bincike kana bin da haddasa fada a tsakanin ’yan Shi’a da ’yan sanda a ranar Litinin din a Abuja. A wata sanarwa da Kakakin Jam’iyyar PDP ta kasa, Kola Ologbondiyan, jam’iyyar ta ce bincike kan hakikanin abin da ya jawo lamarin zai iya gano abin da ya jawo hatsaniyar da ta yi kusan dakatar da komai a tsakiyar birnin.

A daina take hakkin ’yan Shi’a – Amnesty

kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta bukaci Gwamnatin Tarayya cewa kada ta hana wa mutanen kasar nan hakkinsu na yin zanga-zangar lumana Daraktar kungiyar a Najeriya, Misis Osai Ojigho, ta nuna rashin jin dadinta kan hana ’yan Shi’a zanga-zanga a Abuja a jawabin da ta fitar a ranar Talata.

Ojigho ta ce ’yan Shi’ar sun yi taron zanga-zangar kan ka’ida a birnin don neman a sako shugaban nasu daga hannun gwamnati, duk da cewa akwai rahotannin cewa sun jefi jami’an tsaron, amma dai hakan bai bayar da damar a watsa musu ruwan zafi da barkonon tsohuwa ba.

Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta saki Zakzaky da matarsa, sannan ta binciki kisan da aka yi a ranar 12 zuwa 14 ga watan Disamban shekarar 2015 a garin Zariya.