Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta bankaɗo wata haramtacciyar masana’antar man gyaɗan bogi, tare da cafke mutane uku da ake zargin suna da hannu a harkar.
An gano haramtacciyar masana’antar ce a wani fili da aka kewaye da katanga a titin Mamadi, a yankin Maraban Jos da ke Kaduna.
Wannan samame da jami’an sashen leƙen asiri na rundunar suka gudanar ƙarƙashin jagorancin SP Sani Bello, ya gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar 5 ga Mayu bayan samun bayanan sirri.
- An gabatar da sabbin shaidu kan Nnamdi Kanu
- Mazauna gari sun kori Boko Haram bayan kashe kyaftin ɗin soja
Mai magana da yawun ’yan sanda na jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa waɗanda aka kama a masana’antar sun haɗa da Zailani Shuaibu, mai shekaru 33, wanda ake zargin shi ne mamallakinta, da Nasiru Usman mai shekaru 24, da kuma Salisu Usman mai shekaru 49 – dukkansu mazauna Maraban Jos ne.
A cewarsa, ’yan sanda sun samu duro biyu maƙare da kayan aikin sarrafa man, da jarkoki 15 masu nauyin lita 25 na man da ba a kammala tacewa ba, sai jarkoki biyu da ke ɗauke da man gyaɗa na bogi da aka gama tacewa, da kuma duro guda mai kyau.
DSP Hassan ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya jaddada ƙudirin rundunar na kare lafiyar jama’a da kuma kawar da ayyukan laifi a cikin al’umma.
Haka kuma, ya buƙaci mazauna da su ci gaba da lura da abin da ke faruwa a yankunansu domin kai rahoton motsin da ba su gamsu da shi ba zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.