Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta sake lashe gasar Zakarun Turai bayan ta lallasa Paris Saint-Germain da ci daya mai ban haushi.
Karo na shida ke nan Bayern Munich ta ci kofin wanda rabonta da samu tun a kakar 2013 lokacin da ta kafa tarihin cin gasanni uku a shekara guda.
“Ban taba jin dadin kasancewa da kungiyar ba kamar yau. Hansi Flick ya taimaka kwarai tare da ma’aikatansa na horaswa. Kokarin kowa da kowa ne”, inji gola kuma kyaftin dain Bayern, Manuel Neuer.
A minti na 59 Kingsley Coman ya zura kwallo a ragar PSG da kai, wanda daga shi ba a kara cin wani kwallo ba har aka tashi wasan karshen a filin wasa na Estadio da Luz a birnin Lisbon na kasa Portugal.
PSG ‘yar kasar Faransa, ta yi burin daga kofin gasar Zakarun Turai din ta 2020 kasancewarsa karon farko da ta kai washen karshe a tarihin gasar mafi girma a nahiyar Turai.
Amma Coman mai shekara 35, wanda tsohon dan wasanta ne ya kawo mata cikas a wasan karshen da aka buga ba tare da ‘yan kallo ba saboda annobar coronavirus.
— Bayern Munich ta sake kafa tarihi
Da nasarar Bayern Munich a ranar Lahadi, Bayern Munich ta sake kafa tarihin lashe gasanni uku a shekara guda da suka hada da Bundesliga da Kofin Kasar Jamus da kuma ta na Zakarun Turai.
A 2013 lokacin da Hansi Flick ke horasa da ‘yan wasan Bayern Munich ta fara cin gasanni uku a shekara guda.
A bana (2020) ta maimaita tarihin karkashin Jupp Heynckes a gasar ta aka fara a 2019 amma annobar coronavirus ta sa aka tsawaita shi zuwa 2020.
Yanzu Bayern ta shiga jerin kungiyoyin da suka fi yawan kofin gasar wadda AC Milan ta ci sau 13, sai Real Madrid sau bakwai sannan Liverpool wadda ta daga kofin bara a karo na shida, wadda Bayern Munich ta koma ta a yanzu.
Yanzu Bayern ce ta uku a jerin kungiyoyin da suka taba lashe gasar Zakarun Turai. AC Milan ta ci gasar sau 13, sai Real Madrid sau bakwai sannan Liverpool wadda ta daga kofin bara a karo na shida.
— Hakar PSG bai cimma ruwa ba
Kamar yadda aka ambataw, 2020 shi ne kakar ta PSG ta fi haskawa a tarihin gasar Zakarun Turai.
PSG ba ta taba kai wa wasan karshe be tsawon tarihinta a gasar sai a wannan karon, wanda ta yi burin daga kofin domin cika tarihi.