Zuwa shekaranjiya Laraba an samu kungiyoyi hudun da suka haye matakin kusa da na karshe Semi-Fainal a gasar Zakarun Turai.
Kungiyoyin da suka kai wannan matsayi sun hada da kulob din FC Barcelona da ke Sifen da Liberpool da ke Ingila da Ajad da ke Holland da kuma Tottenham da ke Ingila.
FC Barcelona dai ta kai wannan matsayi ne a ranar Talata bayan ta lallasa kulob din Manchester United da ci 4-0 gida da waje yayin da Ajad kuma ta doke Jubentus da ci 3-2 wato gida da waje. A shekaranjiya Laraba kuma kulob din Tottenham ya doke na Manchester City da ci 4-4 amma saboda Tottenham ta fi yawan zura kwallaye a gidan City ne ya sa ta haye mataki na gaba duk da sun yi canjarasa (4-4). Sai kuma wasan da kulob din Liberpool ya lallasa na FC Porto da ke Fotugal da ci 6-1 (gida da waje).
Don haka kungiyoyi hudun da suka rage za su kece raini ne kamar haka: A ranar Talata 30 ga Afrilu za a yi wasa a tsakanin kulob din Tottenham na Ingila da Ajad na Holland da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya sannan washegari Laraba wato 1 ga Mayu, Barcelona za ta karbi bakuncin kulob din Liberpool. Shi ma wasan zai gudana ne da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya.
Sai wasannin zagaye na biyu da za a yi kamar haka: A ranar Talata 7 ga Mayu, kulob din Liberpool zai karbi bakuncin FC Barcelona yayin da a ranar Laraba 8 ga Mayu kuma za a yi wasa zagaye na biyu a tsakanin kulob din Ajad da Tottenham. Kungiyoyi biyu da suka samu nasara a wasannin (gida da waje) ne za su kai karshe wato Fainal.
Kulob din Tottenham ne kadai bai taba lashe wannan gasa ba a tarihi hasali ma wannan shi ne karon farko da ya kai semi-fainal, yayin da Liberpool da FC Barcelona suka taba lashe gasar sau biyar-biyar. Kulob din Ajad ma ya taba lashe wannan kofi a shekarun baya.
Yanzu dai masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda wasannin za su kaya.