Sadiq Abdullahi Umar, matashin da ya wakilci Najeriya a musabakar Alkur’ani a ciki da wajen kasar, ya riga mu gidan gaskiya.
A hirar da Aminiya ta yi da wani dan uwan marigayin mai suna Muhammad Kabiru Makarfi, ya ce “Malam Sadiq ya rasu ne a Kasar Sudan bayan wata ‘yar rashin lafiya kimanin kwanaki 26 da komawarsa daga Kano.
- Salah ya sabunta kwantaragin ci gaba da zama a Liverpool
- LABARAN AMINIYA: Kungiyar Kwadago Ta Kira Zanga-Zanga Kan Yajin Aikin ASUU
Marigayi Sadiq ya rasu yana shekaru 26 da haihuwa, ya kuma bar mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwa da kuma dangi.
Tuni aka yi jana’izarsa a Sudan kamar addinin musulunci ya tanadar.
Kafin rasuwarsa, mahaddacin shi ya lashe musabakar Alkur’anin da aka yi a Kasashen Kuwait da kuma Qatar.
Shi ne kuma zakaran musabakar da aka yi a Kasar Zanzibar a watan Maris na shekarar 2022.
Baya ga wannan, marigayin ya samar da kafofin koyar da karatun Alkur’anin ta intanet a tashar You tube.