Dan kasar Africa ta kudu zakaran gasar olympics Oscar Pistorius, wanda kotu ta yanke wa hukuncin shekara 13 ya kai hukumar gidan yarin kasar kara a kotu.
Tsohon zakaran ya kai hukumar kula da gidajen yari ta kasar ne gaban alkali yana bukatar kotu ta tilasata mata zaman sauraron neman afuwa a bisa tsarin doka.
Lauyansa Julian Knight ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da kamfanin diallancin labarai na AFP a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa, sun shigar da kara ne domin Osca ya cancanci a yi masa afuwa bisa la’akari da shekarun da ya yi a jarun.
A cewarsa. “karar ba ta na nufin dole sai an yiwa Oscar afuwa ba ne, amma a yi zaman sauraron cancantrasa shi mu ke nema”.
Sannan ya ce, Kotun ba ta sa ranar sauraron karar ba, daga nan kuma Lauyan bai kara cewa komai a hirar.
Osca Pistorious shi ne gurgu maras kafafu na farko da ya shiga gasar tseren wasannin Olympics na nakassasu, ya kuma ciwo wa kasarsa Afirka ta Kudu lambobin yabo a shekarun 2011 da 2012.
Wata kotu a kasar ta yanke masa hukuncin shekarun 13 ne a gidan yari sakamakon samun sa da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp a shekarar 2013, inda ya harbe ta da bindiga a gidansu, a bisa kuskuren barawo ne, a cewarsa.
A bisa dokar Afirka ta Kudu kafin a yi wa fursuna afuwa, sai ya yi akalla rabin wa’adin hukuncin da kotu ta yanke masa.
Sannan wajibi ne ya kasance laifinsa na farko, an kuma shaide shi da kyakkyawan hali a yayin zamansa.