Wani dan sanda ya rasu lokacin yake kokarin hana gasar fadan zakaru wadda ba a halatta ta ba, inda zakaran da ya yi kisan yana da farata kamar reza a kafarsa da yake amfani da su wajen kare kansa.
Dan sandan mai suna Laftana Christian Bolok ya shiga tsakiyar gasar fadan zakarun ne a gundumar Arewacin Samar a kasar Philippines, saboda an haramta gasar.
Zakaran da ya yi kisan ya yi amfani farcen kafarsa ne wanda ya zama kamar wani makami, kamar yadda wani dan sandan Lardin Arnel Apud ya sanar.
Gasar fadan zakaru wadda aka fi sani da ‘Tupada’ ta shahara a kasar Philippines inda ake sanya kudi don gasar a tsakanin zakaru biyu da suke fafatawa.
An dakatar da gasar fadan zakaru na wani lokaci bayan bullar cutar coronavirus saboda hada taron jama’a lokacin da ake gudanar da gasar.
Mista Apud ya ce: “Wannan ba karamin rashin sa’a ba ne, yadda dan sandan ya rasa ransa, ta yadda ba zan iya yin karin bayani ba.
“Da farko ban amince ba lokacin da na samu rahoton abin da zakaran ya yi amma wannan shi ne karo na farko a shekara 25 a matsayina na dan sanda da na samu rahoton gasar fadan zakaru ta jawo kashe dan sanda,” inji shi.
A lokacin da shugaban ’yan sandan lardi ke ganawa da manema labarai ya bayyana takaicinsa kan rashin abokin aikinsa wanda ya sadaukar da rayuwarsa a kan aiki.
Shugaban ya bayyana rashin jin dadinsa game da rasuwar Laftana Bolok sannan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalansa da ’yan uwansa.
Ofishin ’yan sandan Lardin Northern Samar ya yi matukar nuna takaicinsa kan rasuwar Laftana Christian Bolok wanda ke kula da ofishin ’yan sanda na birnin San Jose kuma ya sadaukar da rayuwarsa kan aiki.
An kama mutum uku da zakaru biyu da suke gasar a birnin San Jose inda Laftana Bolok yake. ’Yan sanda sun kama wadansu mutum uku da ake zargi sannan ana kokarin nemo wadansu.
Jami’an ’yan sanda sun kama zakaru bakwai baya ga zakarun da suke fadan inda ake zargin an sanya kudin da suka kai Fam 8.74 (kwatankwacin Naira 4,344 kenan).
A watan Agusta a Lardin Samarta Arewa an gargadi masu shirya gasar fadan zakaru ta haramtacciyar hanya bayan samun mutum hudu dauke da cutar Coronavirus.