✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaidu: Dan Najeriyan da ya rage a Champions League

A ranar Laraba ce za a fafata wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila da FC Porto da Portugal a wasan dab da…

A ranar Laraba ce za a fafata wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila da FC Porto da Portugal a wasan dab da na kusa da na karshe na Gasar Zakarun Turai.

Sai dai hankalin masoya kwallon kafa a Najeriya ya karkata kan dan wasan Najeriya daya da ya rage a gasar, Zaidu Sanusi.

Zaidu dan asalin Jihar Kebbi ne da ke Arewacin Najeriya, wanda FC Porto ta sayo daga kungiyar Santa Clara a farkon kakar bana.

Ya buga dukkannin wasannin da kungiyar ta buga a Gasar Zakarun Turai, inda ya zura kwallo daya a wasansu da Marseile.

Dan wasan ya fi nuna kwarewa a wasansu da kungiyar Juventus, inda ya hana Cristiano Ronaldo sakat, sannan yakan samu dama ya je gaba ya taimaka wa ’yan wasansu na gaba.

Zaidu Sanusi lokacin da yake kokarin tare Ronaldo a wasansu da Juventus. Hoto: Gettyimages

An haife shi a garin Jega, a ranar 13 ga Yunin 1997, yanzu yana da kimanin shekara 23 ke nan.

A yanzu dai shi kadai ne dan Najeriya da ya rage a gasar ta Champions League.