✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Zai yi wuya jam’iyyarmu ta PDP ta kafa gwamnati a Filato a 2023’

Ya ce yanzu haka akwai kararrakin ’yan jam’iyyar guda 13, a kotuna daban-daban.

Wani matashi kuma jigo a jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, Idris Umar Zahiri Jos, ya ce zai yi matukar wahala jam’iyyarsu ta iya kafa gwamnati a Jihar a zaben shekara ta 2023.

Matashin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a Jos, babban birnin Jihar ranar Alhamis.

Ya ce duk da ’yan Filato suna son jam’iyyar, amma zai yi wuya ta iya lashe zabe, a Jihar saboda irin rigingimun kararrakin ’yan jam’iyyar har guda 13, a kotuna daban-daban.

 

Zahiri ya ce ba yadda ba a yi ’yan jam’iyar su janye wadannan kararraki ba, amma sun ki janyewa.

Hakan a cewarsa zai iya kai PDP kasa a Jihar a zabe mai zuwa.

Y ace, “Ko jam’iyyar PDP ta shiga zabe ta ci, a zaben shekara ta 2023, za a iya zuwa kotu, a karba.

“Domin ba ayi zabe shugabannin jam’iyyar ba, tun daga matakin mazabu kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ce.

“Wadannan matsaloli ne suke damun wannan jam’iyya a Jihar Filato,” inji shi.

Idris Umar ya yi bayanin cewa a halin da ake ciki, akwai zaben Shugabannin jam’iyyar da ya kamata ayi tun daga matakin mazabu da Kananan Hukumomi har ya zuwa Jiha, amma ba a yi ba.

“Manyan PDP ne matsalar jam’iyyar a Filato. Kuma wannan matsala ce ta sanya PDP bata sami shiga zaben Kananan Hukumomin da aka yi kwanakin baya ba.

“Domin dan wannan jam’iyya ne ya kai kara kotu, kan kada hukumar zabe ta sanya sunayen ’yan takararmu a wannan zabe, domin haramtattu ne.

“Babu shakka idan PDP ba ta kafa gwamnati a Filato ba a zaben shekara ta 2023, ta gama yawo,” inji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su manta da banbance-banbancen da ke tsakaninsu, su hadu kai son magance matsalar.