Diyar Shugaba Buhari, Zahra Buhari-Indimi ta ce yadda mutane suke bankado maboyan kayan tallafin COVID-19 ya nuna cewa ba mahaifinta ba ne matsalar Najeriya.
Zahra ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram.
- Diyar Ganduje ta caccaki gwamnati kan zanga-zangar #EndSARS
- Ba za mu yafe wa Aisha Yesufu ba —Zahraddeen Sani
- Bata-gari sun fasa gidan Yakubu Dogara
- #EndSARS: ‘Yan kabilar Ibo mazauna Kano sun ba Kanawa hakuri
“Yanzu mutane sun tabbatar da cewar Buhari ya raba isassun kayan tallafi, don haka ba shi ne matsalar Najeriya ba”, inji Zahra Buhari.
A kwanaki biyu da suka gabata dubban ’yan Najeriya sun yi ta fasa rumbunan da gwamnatocin jihohi suka adana kayan tallafin COVID-19 suna kwashewa.
Jihohin da aka fasa inda aka killace kayan tallafin sun hada jihar da Legas, Filato, Kaduna, Osun, Kwara, Adamawa da Adamawa da sauransu.
A wasu jihohin an samu kayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin raba wa mabukata a gidajen ’yan siyasa.
Wannan ya jawo sanya dokar hana fita a wasu jihohi, domin guje wa afka wa dukiyoyin al’umma kamar yadda hakan ta faru a wasu jihohi.