Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland a Kano ta yanke wa wasu mutasa biyu da aka samu da laifin bata sunan Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje hukuncin bulala 20.
Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Muhammad Gabari, ta kuma yanke wa Mubarak Isa Muhammad da Nazifi Muhammad Bala, da ake fi sani da nique Pikin, hukuncin shara, ciki har da wanke bandakunan kotun na tsawon kwana 30.
- Mata ’yan majalisa na so a nada mace Ministar Tsaron Najeriya
- An kai wa magoya bayan Atiku hari lokacin da suke lika fastarsa a Ribas
An dai samu mutanen biyu ne da laifin bata sunan Ganduje a wani bidiyon barkwanci da suka wallafa a shafinsu na TikTok, a kwanakin baya.
Tun da farko dai mutanen sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa na bata suna da kuma kokarin tayar da zaune tsaye.
A cewar takardar kunshin tuhumar da ake musu, matasan a cikin bidiyon barkwancin sun yi zargin cewa ba yadda za a yi Gwamnan na Kano ya ga wani fili ba tare da ya sayar da shi ba, sannan yana yawan barci.
A yayin zaman kotun na ranar Litinin, Mai Shari’a Gabari ya umarci masu laifin da su biya tarar N10,000 kowannensu, sannan su biya wata N10,000 saboda tayar da zaune tsaye.
Kazalika, kotun ta umarci masu laifin da su wallafa wani sabon bidiyo a kafafen sada zumunta suna ba Gandujen hakuri a cikinsa.