Zaftarewar kasa da ambaliya a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa mutuwar mutum 18 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
Ma’aikatan kashe gobara ta kasar Brazil ta tabbatar da mutuwar mutum 18 sakamakon ifti’ain, amma ba ta bayar da alkaluman wadanda suka jikkata ko suka bata ba.
- PSG ta doke Real Madrid da ci daya mai ban haushi
- Almundahana: Kotu ta kwace gidajen mai 10 a hannun wani soja
Lamarin ya faru ne a a wani yanki da masu yawon bude ido ke yawan ziyarta a tsaunukan birnin Rio.
Ma’aikatar ta ce ma’aikatan kashe gobara 180 da sauran ma’aikatan ceto ne ke aikin ceto a wurin da abin ya faru a tsaunukan Petropolis, inda aka binne sarkin Brazil na karshe Pedro II, mai tazarar kilomita 68 daga arewacin birnin Rio.
“An aike da tawaga ta musamman da motoci da jiragen ruwa domin gudanar da bincike da ceto mutanee,” inji sanarwar.
Majalisar birnin ta ayyana “dokar ta-baci” a yayin da aka yada hotuna gidaje da motocin da suka lalace a sakamakon ibtila’in.
Shaguna da dama sun cika makil da ruwa sakamakon ambaliyar da ta shafe titunan tsakiyar birnin Rio mai dimbin tarihi.