Kungiyar Kwadago (NLC) reshen Jihar Kano ta janye yajin aikin gargadin kwanki ukun da ta yi yunkurin shiga a ranar Alhamis, bayan zaftare albashin watan Maris na ma’aikatan jihar da gwamnatin Kanon ta yi.
NLC ta janye ne bayan samun masalaha tsakaninta da gwamnatin jihar.
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake da fadawansa
- An nada dan ‘Shugaban Kasar Nijar’ Ministan Mai
- Babu hujja a kyale talaka cuta ta kashe shi —Dokta Amina
- Ana zargin Tambuwal da haddasa rikici a jam’iyyar PDP
Yarjejeniyar ta bayyana cewa “Albashin watan Maris da aka zaftare za a dawo shi a watan Afrilu ko Mayun, 2021, ya danganta da kudin da Gwamnatin Tarayya ta turo.
“An kafa kwamiti tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago don tattauna matsalolin da ma’aikata ke fuskanta.
“Dukkan wasu kudade na wadanda suka yi ritaya daga aiki za a saka su a hukumomin da suka dace.
“Yajin aikin gargadi na kwana uku da zai fara a ranar Alhamis 8 ga watan Afrilu, da kuma zanga-zangar lumana da za a yi ranar Litinin 12 ga Afrilu, an janye su baki daya,” kamar yadda aka bayyana cikin yarjejeniyar.
Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Jihar, kwamishinonin Kudi, Kananan Hukumomi d na Yada Labarai, sai shugabanin kungiyar ma’aikata da sauransu.
Bayan ziyartar wasu ofisoshin kananan hukumomi da wakilinmu ya yi, ya ganewa idanunsa yadda ma’aikata suka koma bakin ayyukansu bayan janye yajin aikin.
Cikin satin da ya gabata ne Aminiya, ta rawaito Gwamnatin Kano tana bayyana kudurinta na daina biyan mafi karanci albashi, tare da gaza biyan albashin watan Maris saboda rashin samun isassun kudi daga gwamnatin tarayya.
Amma gwamnatin jihar ta musanta cewar za ta daina biyan mafi karancin albashi na N30,000.
Har wa yau, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da rage kashi 50% na albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar.