Akalla ’yan sanda 23,000 ne za a tura domin samar da tsaro a zaben cike gurbi mai zuwa a Karama Hukuamr Bakura, Jihar Zamfara.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Usman Nagogo, ya sanar da haka tare da ba wa jam’iyyun siyasa tabbacin isasshen tsaro domin gudanar da zaben cikin aminci.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce a shirye-rundunar take ta sa kafar wando da duk wanda ya nemi kawo wa zaben cikas.
“Wannan zaben cike gurbi ne da dan Majalisar Dokokin Jihar, mun riga mun ayyana wurare masu hadari, kuma za a girke jami’an tsaro domin kar bata-gari su samu wata kafa.
“Muna kira ga ’yan siyasa su kiyaye dokokin zaben kuma kowane dan kasa mai bin doka zai samu damar kada kuri’a ba tare da wata matsala ba”, inji shi.
Jihar Zamfa na fama da matsalar tsaro ta ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wanda ya raba dubban mutane da garuwansu da gonakinsu, baya ga asarar rayuka da dukiyoyi.
A nata bangare, Kwamishinanr Zabe a Jihar Zamfara, Asmau Maikudi ta wajibi ne duk masu kada kuri’a su kiyaye dokokin COVID-19 a lokacin zabe.
Ta ce tuni ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a jihar ya riga ya karbi muhimman kayan zabe, kuma zai gayyaci masu ruwa da tsaki su shaida yadda za a raba kayan.