✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Tinubu alamar nasara ce ga Najeriya —Akpabio

Akpabio ya ce lashe zaben da Tinubu ya yi wata alamar nasara ce ga Najeriya.

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana nasarar Bola Tinubu ta lashe zaben Shugaban Kasa, a matsayin alamun nasara ga kasar nan.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaransa, Mista Jackson Udom, ya fitar ranar Laraba a Uyo.

Udom ya ruwaito Akpabio na cewa nasarar da Tinubu ya samu ta nuna karbuwarsa a fadin kasar nan baki daya.

Akpabio, wanda kuma shi ne zababben Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, ya ce nasarar da Tinubun ya samu kamar yadda INEC ta bayyana, ya tabbatar da karbuwarsa a fadin kasar.

“Bola Tinubu mutum ne wanda aka gwada kuma amintacce wajen aiki.

“An gwada shi a Jihar Legas kuma ina da kwarin gwiwa cewa zai yi wa ’yan Najeriya aiki fiye da abin da ya yi a baya.

“Yana da kwarewar da ake bukata don kai wannan kasa zuwa mataki na gaba a cikin harkokin kasa da kasa,” in ji shi.

Akpabio ya ce daga ranar 29 ga watan Mayu ne za a fara sharbar romon dimokuradiyyar Tinubu.

“Ina taya shugabanni da mambobin jam’iyyarmu murnar wannan nasarar da muka samu,” in ji shi.