Hukumar INEC ta ce tana nan kan bakanta na farawa da zaben Shugaban Kasa a zaben shekarar 2019 kamar yadda jadawalin zaben ya nuna.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja kamar yadda hukumar ke yi lokaci bayan lokaci.
Majalisun Tarayya a kwanakin baya sun gabatar da wani kuduri da ya yi canje-zanje a jadawalin zaben, inda suka bukaci a fara da zabensu, sai na gwamnoni da ‘yan majalisar jiha kafin na Shugaban Kasa.