✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Sanata: Kalubalen da ke gaban Tambuwal

Akwai masu ganin Gwamna Tambuwal zai iya shan kasa.

Hukumar Zabe ta Kasa ta sa Asabar din makon gobe don gudanar da zaben da aka samu tsaiko a zabubbukan da suka gabata da suka hada da na Majalisar Dokoki ta Kasa da na gwamnonin Kebbi da Adamawa da sauransu.

A Jihar Sakkwato, ba wata kujerar sanata da aka bayyana wanda ya yi nasara ciki har da biyun da suka fi daukar hankali, wato wadda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ke nema ta Sanata da wadda Sanata Aliyu Magatakarda ke son sake komawa don wakiltar yankinsa.

A cikin kujeru uku na Sanata Jam’iyar PDP ce ke gaban APC a kujera biyu, inda Aminu Tambuwal ke gaban Sanata Ibrahim Danbaba da ke kai a yanzu da kuri’u 7,859 a yankin Sakkwato ta Kudu, sai Shu’aibu Gwanda Gobir ke gaban Alhaji Ibrahim Lamido da kuri’a 2,059 a Sakkwato ta Gabas.

A yankin Sakkwato ta Arewa Sanata Wamakko na APC ne ke gaban Mataimakin Gwamnan Jihar, Maniru Dan’iya da kuri’a 11,732.

A kujerun Majalisar Wakilai 11, APC ce kan gaba da kujera 8 yayin da PDP ke da kujera 3.

A jawabinsa ga magoya bayansa a taron masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar da aka gudanar, Gwamna Tambuwal ya yi amfani da wani salon kwantar da hankalin magoya bayan, inda ya ce, dan takarar gwamnansu Malam Sa’idu Umar Ubandoma ya fadi zabe.

Ya jajanta wa magoya bayansu tare da cewa mutanen Sakkwato PDP suka zava a zaben Gwamna “Amma aka ga wani abu daban ya fito a matsayin sakamakon zabe, mu Musulmi ne da muka karbi kaddara.

“Ina jawo hankalinmu kada a shige cikin gidaje ana abu kamar juyayi don abin da ake so a samu ba a same shi a lokacin ake bukata ba, mun samu jarrabawa a wannan yaki da muka fito.

“Muna sanar da ku duk matakan da suka kamata a dauka na ganin abin da aka kwata ya dawo hannunmu muna kansa, mu ci gaba da zama amintattun juna kada a zargi wani cewa wane bai yi daidai ba.

Abu ne na Allah Shi zai samar mana fansa, kowa ya san abin da aka yi a Sakkwato,” in ji Gwamna Tambuwal.

Shugaban Jam’iyar PDP a Jihar, Alhaji Bello Aliyu Goronyo shi ma ya kwantar da hankalin mutanensu, inda ya ce sun dauki matakan da suka kamata don ganin an yi nasara a kotu kan kujerar da aka kwace masu.

Ya ce, “Akwai zaven da ya rage da za a yi a ranar 15 ga watan nan, mun dauki duk matakan da suka kamata don samun nasara.”

A bangaren sabon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Ahmad Aliyu bayan ya karbi takardar shaidar lashe zabe ya kara wa magoya bayansa kaimi cewa, su fito su zabi Jam’iyyar APC a zaben da za a gudanar domin kara samun nasara a dukkan matakai.

Alhaji Ahmad Aliyu ya kara tabbatar da alkawarin da ya daukar wa mutanen jihar lokacin yakin zabe na yin mulkin jihar cikin adalci.

Zababben Gwamnan ya ce ba zai ci amanar al’ummar Sakkwato ba kuma ba za a hada baki da shi a ci amana ba, “Zan tabbatar da samar da tsaro da yi wa jama’a da addini aiki,” in ji shi.

Sai ya yi kira ga abokan adawa da suka yi takara tare su zo a hada kai don ciyar da Jihar Sakkwato gaba.

Wasu masu sharhi na ganin Jam’iyyar PDP na iya rasa kujerun gaba daya a zaben da za a yi, ganin yadda APC ta samu nasara a zaben Shugaban Kasa da kuma Gwamna wanda shi ne mafi muhimmanci a jihar, duba da yawan magoya bayan PDP jikinsu na iya sanyi su kasa samun karsashin yin jayayyar da za ta kai su da nasarar kujerun da suke kan gaba.

Sai dai wasu na ganin PDP za ta fito da karfi domin tabbatar da nasararta.

Wasu na ganin Gwamna Tambuwal na fuskantar qalubale ne ganin shi ne jagoran PDP a jihar, hakan ya sa hankalin dukkan ’ya’yan Jam’iyyar APC na kansa don ganin an kayar da shi a kasa duk da ya ba da tazara ga abokin karawarsa.

Akwai masu ganin Gwamna Tambuwal zai iya shan kasa ne domin mafi rinjayen rumfunan zaben magoya bayan APC sun fi karfi a wurin.

Sai dai masu ganin Gwamna Tambuwal zai iya samun nasara suna cewa zai yi wuya dan takarar APC ya kamo shi lura da tazarar kuri’u da ya ba shi, sannan ya kware wajen yakin
sunkurun siyasa.