Dan takarar Gwamnan Jihar Ondo karkashin jam’iyyar PDP, Eyitayo Jegede ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda tangardar na’urar tantance masu zabe ta card reader ta jawo tsaiko kafin kada kuri’arsa.
Rahotanni dai sun nuna Eyitaye Jegede ya ziyarci mazabarsa tun misalin karfe tara na safe inda ya tsaya kusan sa’o’i biyu a kan layi kafin ya kada kuri’a.
Sai dai an sami tangarda lokacin da ya zo kada kuri’a inda na’urar ta ki tantance shi.
Dan takarar ya kuma koka kan yadda tangardar na’urar ke kawo tsaiko a sassa da daman na jihar, ko da yake ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa shi ne zai lashe zaben.
Jegede, ya ce, “Yanayin yadda zaben ke gudana abu ne mai kyau. Masu zabe suna bin tsari yadda ya kamata, sun fito sosai amma abin takaici INEC ce take kawo yawancin matsalolin da ake fuskanta.”
Daga nan sai ya shawarci hukumar kan ta gaggauta shawo kan matsalolin na’urorin domin kauce wa kawo tarnaki ga nasarar da aka samu ya zuwa yanzu.