Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance ne kai tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa.
Shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, ya jaddada cewa zaɓen “Tsakanin Jam’iyyar APC ne da ’yan Najeriya,” yana mai nuni da wahalar da talakawa ke fuskanta a ƙarƙashin mulkin APC.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai don magance abin da ya kira “wahalar da aka kawo mana da gangan.”
Damagum ya kuma yi tsokaci kan sauya sheƙar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon Gwamna, Ifeanyi Okowa, tare da mambobin majalisar zartarwarsu, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
- ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani
A hirarsa da tashar talabijin ta Channels, Damagum ya nuna rashin jin daɗi, yana mai cewa PDP ta kasance mai matuƙar goyon baya ga Jihar Delta kuma ba ta cancanci irin wannan siyasar ba.
Amma duk da sauya sheƙar, ya tabbatar da juriya da kuma ƙarfin PDP.