✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakataren Jam’iyya: Damagum ya amince da matsayar gwamnonin PDP

Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami'an jam'iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya…

Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa.

Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas za su zaɓi cikakken sakatare wanda Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar zai amince da shi.

Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke kan wanda ya cancanci ya riƙe muƙamin tsakanin Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, ta ba jam’iyyar ikon yanke shawara kan shugabanninta.

Sai dai a wata takarda da Alhaji Gurama Bawa, jami’in gudanarwa na mukaddashin shugaban jam’iyyar ya fitar, ta ce Setonji Koshoedo, Mataimakin Sakatare na Ƙasa (DNS), yanzu shi ne Mukaddashin Sakatare na Ƙasa na babbar Jam’iyyarmu har sai an sanar da wani abu.

Takardar ta kuma roƙi ma’aikatan jam’iyyar da su ba sabon mukaddashin sakataren goyon baya wajen gudanar da ayyukansa.

Takardar ta ce: “Dangane da abin da ke sama, duk wasiƙun jam’iyyar ya kamata a tura su ga Hon. (Arch) Setonji Koshoedo.

“An roƙe ku da ku ba shi duk goyon baya da haɗin kai da ys dace a matsayinsa na Mukaddashin Sakatare na Ƙasa na babbar Jam’iyyarmu.”