Kotun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) a ranar Talata ta yi watsi da karar da Mahamane Ousmane ya shigar yana kalubalantar nasarar da Mohammed Bazoum ya samu a zaben Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar.
Kotun dai ta yanke hukuncin ne a kan zaben da aka gudanar a kasar shekarar 2021 da ta gabata.
- Buhari da Ministoci 7 za su ziyarci birnin Madrid
- Malamin coci ya yi wa yarinyar da ta je ya yi mata addu’a fyade
Zaman shari’ar karkashin Mai Shari’a Atoki, ya gudana ne ta bidiyo, inda bayan da mai shari’a ta karanto bayanai kan karar da Ousmane ya shigar da kuma nazarin da kotun ta yi a kan batun, daga bisani ta yi watsi da karar saboda rashin gamsassun hujjoji.
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a gaban lauyoyin bangarorin biyu, wato Barista Abuobakar Sulaiman mai kare wanda ya shigar da kara, da kuma Barista Souley Dagouma mai kare wanda aka yi karar sa.
Daga cikin zarge-zargen da Ousmane ya shigar don neman kotu ta soke nasarar da Shugaba Bazoum din ya samu, har da zargin tafka magudi yayin zagaye na biyu na zaben da ya gudana a Fabrairun 2021, da rashin bin doka da dakile masa hanyar sadarwa lokacin zaben da sauransu.
Sai dai Mai Shari’a Atoki ta bayyana gamsuwar kotun kan hujjojin da bangaren Shugaba Bazoum ya gabatar wajen kare kansa wanda hakan ya sa kotun yanke hukuncin yin watsi da karar Ousmane.
Idan dai ba a manta ba, Shugaba Mohamed Bazoum ya lashe babban zaben Kasar Nijar da ya gudana a bara ne bayan samun kashi 55 cikin 100 na baki daya kuri’un da aka kada, yayin da abokin hamayyarsa, Mahamane Ousmane ya samu kashi 44.34.