✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Mataimaki: Wike ya zama abokin takarar Atiku a PDP

Hakan ya biyo shawarar da Kwamitin da jam'iyyar ta kafa ya bayar

A kokarinsa na kawo karshen tirka-tirkar neman Mataimaki ga dan takararta na Shugaban Kasa, wani kwamitin da jam’iyyar PDP ta kafa ya ba da shawarar daukar Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.

Hakan na zuwa ne bayan kwamitin ya tantance wanda ya fi cancanta da mukamin daga cikin ,yan takara uku da suka yi zawarcin mukamin.

Aminiya ta kalato cewa, Gwamnan na Ribas shi ne ya yi nasarar a zaben da kwamitin ya gudanar a tsakankin ‘yan takarar, zaben da ya aka gudanar a hedkwatar PDP da ke Abuja.

An kafa kwamitin ne don ya yi nazarin rahoton kwamitin Janar Aliyu Gusau.

Tun farko, kwamitin Gusau ya ba da shawarar a dauki wanda zai yi Mataimakin a tsakanin Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa da na Ribas, Nyesom Wike da kuma Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom.

Bayanai sun tabbatar cewa, Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, shi ne wanda ya kafa kwamitin shawarar a ranar Talata tare da ba shi damar soma aiki nan take.

Inda shi kuma kwamitin ya sauke nauyin da aka dora masa yayin wata ganawar sirri da mambobinsa suka yi a Abuja.

Majiyarmu ta ce mutum 19 daga cikin mambobi 20 da kwamitin ke da su ne suka hadu wajen gudanar da zaben.

Majiyar ta kara da cewa, mutum 16 daga cikin mahalarta taron su 19 ne suka zabi Gwamnan Ribas a matsayin wanda zai yi wa dan takararta Atiku Abubakar Mataimaki a babban zaben na 2023.

Wike dai shi ne dankarar da ya zo na biyu yayin zaben fid-da gwanin da jam’iyyar PDP ta gudanar a watan jiya a Abuja, wanda Atiku Abubakar ya lashe.

“Sa’ilin da shugaban kwamitin shawarar, Ambasada Umar Shehu Damagum, ya bukaci ‘yan kwamitin masu goyon bayan Wike su daga hannu, sai aka ga mutum 16 sun daga hannunsu, wanda hakan ya nuna nasarar Wike a bayyane.

“Ai ka ga irin rawar da ya taka a zaben fidda gwani. Shugabannin jam’iyya na da kwarin gwiwa a kansa kuma sun zabe shi. Shi ne za a tsayar a matsayin mataimaki ga dan takarar Shugaban Kasa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar,” inji majiyar.

Ta ce nan ba da jimawa ba kwamitin shwarar zai mika rahotonsa ga Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) don mika wa dan takarar Shugaban Kasa.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Gwamna Samuel Ortom na Binuwai, Aminu Tambuwal na Sakkwato, Bala Mohammed na Bauchi, tsoffin gwamnoni Babangida Aliyu na Neaja da Sule Lamido na Jigawa da  Liyel Imoke na Kuros Ribas) da Olusegun Mimiko na Ondo da kuma shugaban marasa rinjaye na Majlisar Wakilai, Ndudi Elumelu da sauransu.

Tun farko, sa’iln da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin, Ayu ya bukaci ‘yan kwamitin da su tabbatar sun kammala aikinsun kafin ranar Juma’a.

Ya ce, Atiku ya yi wa jam’iyyar wasika yana mai neman jam’iyya ta taimaka masa wajen zaben wanda zai zame masa mataimaki.

Ya kara da cewa, sassan jam’iyyar sun samu wakilci a kwamitin da ya yi aikin zaben mataimakin.

Gwamnonin APC sun ki cewa uffan bayan ganawa da Buhari

A hannu guda, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin Jam’iyyar APC ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya jagoranci takwarorin nasa zuwa wajen Buhari.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin jam’iyyar ke ta fadi-tashin tsayar da wanda zai yi wa dan takararta Mataimaki a babban zaben 2023.

Mahalarta taron sun hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Gwamna  Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa, Abdullahi Sule na Nasarawa, Simon Lalong na Filato, Yahaya Bello na Kogi da kuma Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo.

Bayanai sun nuna Bola Tinubu ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ne a matsayin wanda zai yi masa Mataimaki saboda rawar da ya taka wajen yakin neman zabensa.

Aminiya ta tattaro cewa, wasu ’yan jam’iyyar CPC, jam’iyyar da ta ba da gudunmawa wajen kafa APC, na shirin ganawa da Shugaba Buhari domin ba da shawara kan ko a zabi Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ko kuma Ministan Sufurin Jirgen Sama, Hadi Sirika a matsayin Mataimakin Tinubun.

Bayan kammala ganawar tasu da Shugaba Buhari, gwamnonin sun yi tafiyarsu ba tare da yi wa manema labarai wani bayani dangane da abin da suka tattauna ba.

Da kansa Tinubu zai zabi mataimakainsa – Gwamnan Imo

Sai dai kuma, a ranar Talata aka ji Gwamnan Imo, Hope Uzodimma na cewa, Tinubu da kansa zai zabi wanda zai yi masa mataimaki a zaben 2023 amma ba gwamnoni ba.

Gamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa jim kadan bayan ganawarsu da Shugaba Buhari dangane da shirin karbar bakuncin Buhari a jiharsa inda zai kaddamar da wasu manyan ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar.

Ya ce za a yi la’akari da abubuwan da za su kawo wa kasa cigaba da hadin kai da kuma adalci yayin zaben mataimakin sabanin yadda wasu ‘yan jami’iyyar ke tunani.

Dangane da batun cewa APC na shirin daukar Musulmai su zama Shugaban Kasa da mataimakinsa, gwamnan ya ce babu in Kundin Tsarin Mulkin Njeriya ya nuna addini na daga cikin abubuwan dubawa kafin zama Shugaban Kasa ko mataimakainsa.

Ya ci gaba da cewa, “Dunkulalliyar Najeriya muke fata, inda za a bai wa sha’anin shugabanci muhimmanci, inda kuma za a rika la’akari da cancantar shugaban kasa wajen samar da ribar dimokuradiyya da kuma bunkasa Najeriya tamkar sauran kasashen duniya da suka cigaba.

“Ba na son in takaita lamarin shugabanci a Najeriya zuwa ga abin da zai haifar da rarrabuwar kawuna sai dai batun hadin kan kasa maimakon haka, kula da ‘yan uwantaka, samun Shugaban Kasar da zai zama wakili ga kowace kabila da addini, ta yadda a karshe za mu hayi tudun mun tsira.

“Sannan matsayin zaben mataimaki ba ya hannun kowannenmu daga cikin gwamnoni. Dan takarar Shugaban Kasa da kansa zai duba ya ga way a fi cancanta ya ame masa mataimaki. Don haka ba abu ba ne da za mu auna mu yanke a tsakaninmu ba,” inji Uzodimma.

Ba mu yi wata tattaunawar kawance ba – NNPP

Sabanin bayanan da aka yi ta yayatawa a Kafafen Sada Zumunta na Zamni cewa sabuwar Jam’iyyar NNPP na zawarcin kulla kawance da Jam’iyyar Labour (LP), Sakataren Yada Labarai na Kasa na NNPP, Agbo Major, ya ce wannan ba gaskiya ba ne.

“Mu da kanmu muke daukar nauyin dan takararmu na Shugaban Kasa, kuma duk wanda ke sha’awar hada karfi da mu, kofarmu a bude take,” inji shi.

Haka nan, ya ce har yanzu ba su tsayar da wanda zai zama Mataimain Shugaban kasa ba.

Sai dai kuma, an jiyo Jam’iyyar Labour na cewa tana kan tattaunawa da takwararta NNPP karkashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso game da yiwuwar hada karfi wuuri guda don zaben 2023.

An ji hakan ne ta bakin Sakataren Yada Labarai na Kasa na Jam’iyyar Labour din, Kwamred Abayomi Oluwafemi Arabambi, yayin wata tattaunawa da aka yi da shi ran Talata.

Ya ce, Jam’iyyar Labour wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi shi ne dan takararta na Shugaban Kasa, na ci gaba da tattaunawa da NNPP game da batun mataimaki da kuma kawance domin ceto Najeriya.

Kazalika, ya ce suna tsakar tattaunawa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau da kuma sauran masu ruwa da tsaki dangane da takarar Shugaban Kasar.

“Muna kokarin hada tsare-tsarenmu tsakaninmu da Kungiyar Kwadago ta Najeriya da Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Kungiyar Tuntuba ta Kasa, Kungiyoyn Musulmi da Kirista da dai sauransu, don ganin yadda za mu hada karfi da karfe don tunkarar zaben 2023,” inji shi.

Baba Martins, Muideen Olaniyi, John Chuks Azu, Terkula Igidi Da Bashir Isah