Kotu ta ba wa hukumar tsaro ta DSS izinin ci gaba da tsare wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP da hukumar ta cafke a Jihar Kano, har na tsawon kwana bakwai.
- ISWAP da IPOB na cikin kungiyoyin ta’addanci 10 mafiya hadari a duniya —Rahoto
- Za mu kama duk wanda ya dauki makami ranar zabe a Kano —’Yan sanda
Magoya bayan NNPP din da hukumar ta gurfanar ranar Alhamis a gaban Kotun Majistare da ke No-man’s-Land da ke Kano sun hada da wani malamin addini mai suna Isma’il Iliyasu Mangu da kuma dan wasan barkwanci, Sharu Abubakar Tabula, wanda aka fi sani da Habu Tabule.
Wata sanarwa da kakakin DSS, Peter Afunanya ya fitar a ranar Alhamis cewa, an kama Habu Tabule da malamin ne bayan kowannensu ya yi wani sakon murya na tunzura jama’a tare da yadawa a kafofin sada zumunta.
Afunanya, ya tura wa wakilinmu sakon muryar, yana mai kira ga masu yadawa su janye daina, ko su kuma fuskanci fushin hukuma.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari ya amince da bukatar hukumar DSS na ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma domin fadada bincike kan zargin da ake musu na yin kalaman tunzuri da neman tayar da tarzoma a zaben gwamna da ’yan majalisar dokokin jiha.
Daga nan kotun ta dage zaman zuwa ranar 23 ga watan Maris da muke ciki.
DSS ta ce ta girke jami’anta a sauran jihohi da ke fadin Najeriya domin “bibiyar duk wani dan siyasa da ke shirin tunzura mutane gabanin zaben ranar 18 ga watan Maris da muke ciki”.