✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Kaduna: APC ta lashe mazabar Kauru

APC ta samu kuri’u 24,170 daga jimillar kuri’u 59,358 yayin da PDP ta samu 23,591.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ke wakiltar mazabar Kauru, Barnabas Haruna Danmaigona ne ya yi nasara bayan ya doke dan takarar jam’iyyar PDP Yohanna Gandu Chawai a zaben da aka sake gudanarwa.

Baturen zaben, Farfesa Abdullahi Inusa Idris na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya, ya bayyana cewa APC ta samu kuri’u 24,170 daga jimillar kuri’u 59,358 yayin da PDP ta samu kuri’u 23,591.

Da yake bayyana sakamakon zaben a ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke garin Kauru, da misalin karfe 10:25, Farfesa Abdullahi Inusa Idris ya ce don haka, Barnabas Haruna Danmaigona na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

An gudanar da zaben ne a rumfunan zabe 6 na Dandaura 001, Dandaura 002, Dandaura 003, Barwa da Wugama da ke gundumomin Makami da Dawaki.