✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnoni: Jihohin da za a yi gumurzu gobe

A gobe Asabar ce masu jefa kuri’a a jihohi 29 daga cikin jihohi 36 na kasar nan za su fita rumfunan zabe domin zaben gwamnonin da…

A gobe Asabar ce masu jefa kuri’a a jihohi 29 daga cikin jihohi 36 na kasar nan za su fita rumfunan zabe domin zaben gwamnonin da za su jagoranci jihohinsu a shekara hudu masu zuwa.

Kuma ga dukan alamu za a yi gurmuzu a wasu jihohi a zaben na gobe, sakamakon yadda kurar siyasa take kadawa a jihohin.

Misali a Jihar Kaduna za a shawo ta sosai a tsakanin Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i da babban mai kalubalantarsa Alhaji  Muhammad Ashiru Kudan na Jam’iyyar PDP. Gwamna Nasir El-Rufa’i wanda ya dauki mace Musulma daga Kudancin Kaduna inda Kiristoci suke da rinjaye ya fusata mabiya addinin Kirista a jihar wadanda suke ganin abin da ya yi a matsayin tozarta su da kokarin yin watsi da su a siyasance. Sai dai a nasa bangaren Gwamna El-Rufa’i ya ce babu batun addini ko kabilanci a zabin da ya yi, inda ya ce ya kamata a rika fifita cancanta da dacewa a batun siyasa maimakon kabilanci da nuna bambancin addini. Ya ce mataimakiyarsa da ya dauka Hajiya Hadiza Balarabe ya dauke ta ne bisa kwarewa ba tare da lura da addini ko kabilar da ta fito ba.

To amma akwai majiyoyin da suke cewa yadda al’ummar Kudancin Kaduna musamman mabiya addinin Kirista suka mayar da Jam’iyyar PDP tamkar addini ta yadda ba su zaben wata jam’iyya in ba ita ba ne ya sa Gwamna El-Rufa’i ya dauko Hajiya Hadiza a matsayin mataimakiyarsa. Majiyoyin sun ce idan har Gwamnan ya samu nasara a zaben na gobe zai karya lagon siyasar kabilanci da addini da jihar ke fama da ita tun dawowar mulkin dimokuradiyya shekara 20 da suka gabata. Kuma hakan zai sa kabilun Kudancin Kaduna su dawo daga rakiyar jam’iyya daya kacal kamar yadda suka saba. Sun kawo misali da yadda ko dan yankin Kirista ne ya tsaya takara a wata jam’iyya ba PDP ba, ba su zabensa lamarin da suke jin shi ne dalilin da Gwamna El-Rufa’i yanke shawarar dauko Musulma daga yankinsu don mara masa a matsayin mataimakiya.

Sai dai wannan dabara ta dada raba kan al’ummar jihar tare da haifar da zazzafar siyasar addini da kabilanci, ta yadda aka rika zargin kungiyoyin addini da zuga mabiyansu kan yadda za su gudanar da zaben na gobe.

A zaben Shugaban Kasa da aka gudanar makon shekaranjiya ya dan yayyafa wa wutar zazzafar siyasar da ake yi a jihar ruwa, bayan da Jam’iyyar APC ta samu nasara a Arewaci da Tsakiyar Jihar da gagarumar rinjaye. Hakan ya sa wasu kungiyoyin kabilu a Kudancin Kaduna sun fara nuna shakku kan yadda manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo da tsohon Gwamnan Jihar Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Suleiman Hunkuyi suka kasa kawo koda kananan hukumominsu a zaben. An samu wata kungiya da ta ba manyan ’ya’yan na PDP na Arewacin jihar wa’adin awa 24 su bayyana dalilin da suka sa suka gaza kawo mazabu da kananan hukumominsu ga PDP in ba haka ba, mutanen Kudancin Kaduna za su canja salo wajen komawa wata jam’iyya ciki har da APC.

Kuma a farkon wannan mako wani na hannun damar Alhaji Namadi Sambo, Alhaji Sani Sidi, tsohon Darakta Janar na Hukumar NEMA ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC, a wani abu da ake ganin sharar fage ce ga ubangidansa ko kuma akalla alamar ba zai goya wa PDP baya ba a zaben na gobe.

Jihar Kano inda madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya gaza samun koda kujerar dan Majalisar Dokoki ta Kasa a zaben da aka gudanar kusan mako biyu da suka gabata, ana jin a wannan karo sai yadda karfinsa ya kare don ganin ya raba Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ke neman tazarce a kujerarsa.

Kwankwaso da Ganduje dai abokan siyasa ne na sama da shekara 30, kafin su babe a shekara uku da suka gabata.

Kwankwaso wanda ya tsayar da surukinsa Alhaji Kabir Abba, babban burinsa shi ne kawar da Gwamna Ganduje, to amma yadda manyan dakarunsa da suka hada da tsohon Mataimakin Gwamna Ganduje, Farfesa Hafiz Abubakar da Alhaji Aminu Dabo da sauransu suka kaurace masa tare da goya wa Ganduje baya, alama ce da ke nuna cewa da kamar wuya Kwankwaso ya samu nasara a wannan gumurzu.

Kuma ana cikin wannan hali ne a ranar Litinin din da ta gabata, sai Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta soke sunan Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP.

Kotun a karkashin Mai shari’a Lewis Allagoe ta ce zaben fitar da gwanin da aka fitar da sunan Abba K. Yusuf  a matsayin dan takarar jam’iyyar ba ya bisa ka’ida.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne  sakamakon karar da Alhaji Ibahim Al’amin (Little) ya kai gabanta yana kalubalantar zaben fid da gwani da Jam’iyyar ta PDP ta yi inda ya ce ba a gudanar da zaben yadda ya kamata ba.

Alhaji Ibrahim Little ya bukaci a cire sunan Abba K. Yusuf daga jerin ’yan takarar Gwamna a Hukumar INEC, inda ya ce Jam’iyyar PDP ba ta ba shi damar shiga takara ba duk da cewa ya sayi fom don shiga takarar.

Sai dai Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Dokta Rabi’u Sulaiman Bichi ya ce “Jam’iyya ta daukaka kara zuwa kotun gaba kuma hakan ba zai tsayar da mu daga shirye-shiryen zabe ba. Har yanzu dan takararmu shi ne Abba K. Yusuf zai kuma fafata a zaben Gwamna da za a yi a ranar Asabar (gobe).”

Kakakin dan takarar Gwamnan na PDP Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce wancan hukunci na kotu bai shafi dan takararsu ba. “Abin da muke so jama’a su fahimta shi ne wannan kara ba ta shafi dan takararmu Injiniya Abba Kabir Yusuf ba. Kara ce tsakanin Jam’iyyar PDP ta Kasa da ta Jihar Kano da Alhaji Ibrahim Little. Babu sunan Injinya Abba Yusuf a cikin wadanda ake kara haka kuma babu sunansa a hukuncin da aka yanke duk da cewa shi dan Jam’iyyar PDP ne kuma shi ke rike da takarar jam’iyyar a kujerar gwamnan Jihar Kano a shekarar 2019.”

Dawakin Tofa ya zargi Jam’iyyar APC da hannu cikin wannan lamari inda ya ce “Mun yi mamakin yadda tun kafin kotu ta bayyana wannan hukunci sai ga shi batun ya fara fitowa daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta shafinsa na sada zumunta. Wannan ya nuna a fili cewa Jam’iyyar APC na da hannu cikin wannan lamari.”

Madugun Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a wata hira da Rediyon Aminci ya zargi Jam’iyyar APC da shirya wannan lamari saboda tsoron faduwa a zabe da take hange idan har ta kara da Jam’iyyar PDP. “Wannan duk makarkashiya ce da tadiya irin ta siyasa domin Jam’iyyar APC ta hango wa kanta faduwa a zabe shi ya sa take kokarin ganin dan takararmu bai shiga cikin zaben ba. Sai dai wannan abu ba zai yi tasiri ko domin ni na yi imani cewa wannan kiyayya za ta zame mana alheri na gaba.”

Hukumar INEC ta bakin Kakakinta a Jihar Kano Alhaji GarbaLawal ta ce “Idan kotu ta nemi Jam’iyyar PDP ta sake zaben fitar da gwani, ita kuma PDP a rubuto mana to a shirye muke mu je mu sa ido a kan zaben.”

Sai Jihar Bauchi inda wasu jam’iyyun adawa da wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi suka hade kai don kawar da Gwamnan Jihar Mohammed Abdullahi Abubakar na Jam’iyyar APC.

Jihar Bauchi dai a zaben Shugaban Kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa, ta fita daban, inda bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu gagarumar nasara a zaben, Jam’iyyar PRP ce ta lashe manyan mazabun Majalisar Wakila biyu na Bauchi da Katagum da ke jihar.

Sakamakon zabubbukan ya nuna cewa mutane sun zabi abin da suke ganin shi ne ya fi cancanta gare su. Kuma duk da cewa akwai korafe-korafe amma masana na gani zabubbukan suna iya zama matashiya ga yadda zaben Gwamnan Jihar na gobe zai kasance.

Gwamnan Jihar Mohammed Abdullahi Abubakar wanda yake faman shan suka cewa ya gaza tabuka abin a zo a gani a shekara uku na mulkinsa ya tashi haikan ba dare ba rana domin samun nasarar Shugaba Buhari da kuma tasa. Ya samu karin tagomashi lokacin da Shugaban Buhari ya daga hannunsa a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC bayan an rika rade-radin ba shi ne dan takararta ba. Kuma a wannan lokaci ne aka bayar da sanarwar cewa wadansu jiga-jigan Jam’iyyar PDP a jihar su 18 sun koma APC ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar, Ahmadu Adamu Mu’azu da Malam Isa Yuguda da mataimakansu da sauransu. Kuma tun lokacin da suka shiga cikin tafiyar ce suke ta ba da gudunmawa domin ganin Gwamna Abubakar da Shugaba Buhari sun samu nasara.

Sai dai suna cikin wannan gwagwarmaya ce sai ga wadanda ba sa goyon tafiyar Gwamnan fiye da mutum 20 a karkashin jagorancin Wazirin Bauchi Alhaji Muhammadu Bello Kirfi da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da wadanda suka nemi tsaya wa APC takarar Gwamna, Dokta Ibrahim Yakubu Lame  da Kyaftin Bala Jibrin da ’yan takarar Gwamna a Jam’iyyun  APC da PRP da PDP da GPN da PDM suka ce sun hada kai da sauransu  domin su kayar da Gwamna Abdullahi Abubakar a zaben na gobe saboda abin da suka kira gazawarsa.

Alhaji Bello Kirfi wanda ke jagorantar tafiyar ya ce dukansu manufarmu daya ce, ita ce a sallami Gwamna Abubakar daga mulkin jihar. Ya ce babu wasu ayyukan da aka faro aka kare a sama da shekara uku a jihar duk da dimbin kudaden da jihar ta samu daga Asusun Tarayya da sauran hanyoyi da suka haura Naira biliyan 50.

Gamayyar tasu ta kunshi jam’iyyu 33 da ’yan takarar Gwamna 20 inda suka yanke shawarar goya wa dan takarar Jam’iyyar PDP Sanata Bala Muhammad Abdulkadir Kauran Bauchi baya.

Sai dai masu lura da yadda al’amuran siyasar jihar ke gudana sun ce jam’iyyun PRP da PDM da a taron farko aka ambace su a hadakar yanzu ba sunansu a  wannan tafiya.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PRP, Dokta Muhammad Ali Pate wanda jam’iyyarsa ta samu kujerar ’yan majalisa biyu mafiya girma a jihar bai amince a bar wa dan takarar Jam’iyyar PDP ba, wanda ko dan majalisa daya jam’iyyarsa ba ta da shi.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, kafin zaben Shugaban Kasa da wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa, an amince cewa duk jam’iyyar da ta fi samun kujeru a zaben ce za ta bayar da dan takarar Gwamna, amma bayan PRP ta fi PDP kwazo sai aka wargaza wannan tsari. Majiyar ta ce, kila ganin haka  ne ya sa dan takararta na Gwamna Dokta Ali Pate ya ki amincewa da mika takarar ga dan takarar PDP.

A wata hira da manema labarai, Dokta Ali Pate ya ce jam’iyyarsu ta PRP tana cikin duk wani hadaka da za a yi shi cikin gaskiya da adalci domin ci gaban Jihar Bauchi, amma ba ta cikin duk wani hadaka da za a yi shi domin biyan bukatar wadansu mutane.

Dokta Pate ya ce tunda farko sai da suka ce a dauki tsarin da za a bi don zakulo wanda ya fi cancanta ya kasance shi ne dan takarar da zai fi karbuwa wajen al’ummar jihar, ya ce idan aka kwatanta nasarar da jam’iyyarsa ta PRP ta samu a zaben Shugaban Kasa da Majalisar Tarayya zai zama jam’iyyar tana gaba da Jam’iyyar PDP, in an je kotu za ta iya kwato da yawa daga cikin kujerun da yake zargin an yi musu magudi.

Ya ce saboda karbuwar jam’iyyarsu ce ya sa wadanda suka sanya Jihar Bauchi a cikin kunci da rashin aikin yi da talauci suka taru suka hada kai domin ganin sun kawar da Jam’iyyar PRP wacce ita ce mafi karbuwa a jihar.

To amma kuma akwai bayanan da ke cewa wanda ya yi nasara a zaben Majalisar Wakilai a Karamar Hukumar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PRP, Alhaji Yakubu Shehu Abdullahi yana goyon bayan a mara wa dan takarar PDP, don kawar da gwamnatin APC, abin da Dokta Pate ya musanta.

Barista Yakubu Dogara da Wazirin Bauchi suna ta zawarci Yakubu Abdullahi don amincewa da hadakarsu tare da goya musu baya don cimma nasarar kawar da Gwamnan.

Kuma tuni dan takarar Sanatan Bauchi ta Kudu a Jam’iyyar PRP, Barista Lawal Husseini Ibrahim ya nuna goyon baya ga hadakar, lamarin da ake ganin koma baya ne ga Dokta Pate.

Sai dai Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Mohammed Abubakar, Malam Abubakar El-Sadikue ya ce duk wata hadaka da wadansu mutane za su yi ba abin damuwa ba ne gare su, domin al’ummar Jihar Bauchi ne suke da kuri’ar zabensu ko kayar da su a mulki ba wadansu tsirari ba. “Don haka muna neman goyon bayan Allah ne sannan da na al’ummar Jihar Bauchi. Abin da muke dubawa talakan da yake kada kuri’a shi muke neman kuri’a a wajensa, kuma a baya PDP ta ce mu taron yuyuyu ne amma Allah Ya karbi mulki daga hannunta Ya ba mu. Yanzu PDP ce ke neman hadin kan wadansu mutane don a kayar da mu. Don haka ba abin da zai ba mu tsoro muna nema ne a wajen Allah da kuma talakan Jihar Bauchi,’ inji shi.

Ya ce sun yi wannan hadin kai ba su yi nasara ba a zaben Shugaban Kasa, APC ce ta yi nasara, “Don haka muna tare da talakawan Jihar Bauchi, sun san ayyukan da muke yi na inganta rayuwa kamar shimfida hanyoyi da samar da tsaro da ruwan sha da yaki da talauci da sauran ayyuka duk da irin matsin tattalin arziki da Allah Ya jarrabi kasarmu da shi,” inji shi.

Sai Jihar Kwara inda a zaben da ya gabata, Jam’iyyar APC ta yi wa PDP tsirara a kasuwa, kuma a yayin da APC ke son ci gaba da rike nasarar da ta samu a baya, masu fashin baki suna ganin PDP za ta yi kokarin daukar fansa a zaben Gwamna na gobe don fanshe haushin kayen da aka yi wa uban siyasar Jihar Sanata Bukola Saraki.

Sai kuma Sakkwato, inda za a gwada kwanji a tsakanin uban siyasar jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda shi ne jagoran Jam’iyyar APC a Jihar da kuma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, na Jam’iyyar PDP. Tambuwal wanda ya so tsaya wa Jam’iyyar PDP takarar Shugaban Kasa, zai ja daga sosai don ganin akalla ya tsira da kujerarsa ta Gwamna, inda zai fafata da tsohon Mataimakinsa Ahmed Aliyu na Jam’iyyar APC da yake samun goyon bayan Sanata Wamakko.

Jihar Legas ma akwai alamun za a yi gumurzu sosai, ganin cewa PDP ba taba kafa gwamnati a jihar ba bayan dawowa mulkin dimokuradiyya. Jam’iyyar PDP za ta so karya kwarin uban siyasar jihar Sanata Bola Tinubu a wannan karo, musamman ganin Tinubu ya yi amfani da tasirinsa ya hana Gwamna Ambode tazarce a zaben na gobe.

Jihar Oyo ma ga alama za a yi gumurzu a zaben na gobe musamman a tsakanin manyan jam’iyyun nan biyu PDP da APC. Tuni wasu jam’iyyu suka hade don mara wa dan takarar PDP Makinde, sai dai kuma daya daga cikinsu tsohon Gwamnan Jihar Alao Akala ya yi tutsu wa hadakar tasu inda ya koma bayan dan takarar Jam’iyyar APC, Adelabu.

Sannan ga Jihar Ogun da Imo, inda gwamnoninsu masu barin gado suke goyon baya ga ’yan takarar wasu jam’iyyu  maimakon jam’iyyarsu ta APC, nan ma za a yi gumurzu sosai. Gwamna Ibekunle Amosun yana goyon baya dan takararsa a Abdulkadir Akinlade na Jam’iyyar APM, yayin da Rochas Okrocha yake goya baya ga surukinsa Uche Nwosu da ke takara a Jam’iyyar AA. Wadannan jihohin biyu Jam’iyyar PDP ta yi likimo don tsintar dame a kala.

Jihohin Adamawa da Taraba ma akwai alamun za a fafata sosai, Gwamna Jibrilla Bindow yana fama da adawar cikin gida tare da fuskantar kalubale daga Jam’iyyar PDP a zaben na gobe. Cikin masu adawa da Gwamna Bindow har da Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari, wadda Gwamna Bindwo ya kayar da kanenta a zaben fid da gwani, sai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da sauransu da dama. Sannan nasarar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya samu a zaben Shugaban Kasa da ya gabata, ta karfafa gwiwar ’ya’yan Jam’iyyar PDP wadanda suke kokarin jihar ta dawo hannunsu.

Shi kuma dan takarar Jam’iyyar APC a Jihar Taraba Alhaji Danladi Abubakar wanda yake kokarin kwato jihar daga hannun Gwamna Darius Ishaku kotu ta girgiza tafiyarsa bayan da ta yanke hukuncin hana shi takara kan sabanin da aka samu game da ranakun haihuwarsa a hukuncin da ta yanke a wannan mako da muke ciki. Sai dai jam’iyyarsa ta APC ta ce wannan tsohon zance ne da kotu ta magance a baya, don haka ba gudu ba ja da baya wajen fafatawarsa a zaben na gobe. Danladi Abubakar fitaccen dan siyasa ne da ya yi Mataimakin Gwamna ga marigayi Gwamna Danbaba Suntai.

A Jihar Benuwai ma Gwamna Samuel Ortom na Jam’iyyar PDP yana fuskantar kalubale daga dan takarar Jam’iyyar APC Emmanuel Jime, wanda ya sha alwashin kawar da Gwamnan bisa abin da ya kira gaza tabuka abin a zo a gani a shekara kusan hudu na mulkinsa. Jime wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar Sanata George Akume wanda ya sha kaye a zaben Sanatan da ya gabata, ana ganin Akume zai yi kokarin daukar fansa wajen kayar da Ortum a zaben na gobe.

Sai kuma Jihar Filato inda Gwamna Simon Bako Lalong ke fuskantar barazana daga dan takarar Jam’iyyar PDP, Janar Jaremiah Useni.

A zaben 2015, Lalong ya samu nasara ce sakamakon tutsun da sauran kabilun jihar suka yi wa dan takarar PDP da tsohon Gwamnan Jihar Jonah Jang ya tilasta musu daga kabilarsa.

A yanzu da Useni ya fito daga wata kabila ba Berom ba, akwai yiwuwar batun kabilanci ba zai taka rawa a zaben na gobe ba. Sannan nasarar da PDP ta samu a zaben Shugaban Kasa yana iya karfafa mata gwiwa don samun nasara a zaben na gobe.

Gwamna Lalong ya kuma rasa tagomashi a wurin al’ummar Hausawa da Fulani da suka goya masa baya a zaben 2015, saboda gaza cika alkawuran da ya yi musu na samar musu da kayayyyakin inganta rayuwa a yankunan da suka fi rinjaye.

Baya ga wadannan jihohi babu mamaki a samu gumurzu da kuma abubuwan mamaki da za su iya faruwa a zaben na gobe.