Gobe Asabar idan Allah Ya kai mu, za ta zama ranar karshe ta zabubbukan bana, kuma zabubbukan kasa karo na shida, bayan kasar nan ta koma turbar dimokuradiyya a1999. Yau kusan shekara 20 ke nan da sojoji suka hakura wajen daina yin kutse cikin harkokin mulkin kasar nan da sunan juyin mulki. Tun farko Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a jadawalin shirye-shiryen zabubbukan bana da ta fitar kusan shekara guda da ta gabata ta shirya fara yin zaben Shugaban Kasa da na majalisun dokoki na kasa a ranar Asabar 16 ga Fabrairun da ya gabata. Ta kuma tsayar da ranar 2 ga watan nan na Maris ta zama ranar da za ta gudanar da zaben gwamnonin jihohi da na majalisun dokoki na jihohi, amma kwatsam ’yan awowin da suka rage za a fara zaben, sai Shugaban Hukumar INEC na Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya ba da shelar dage zabubbunkan Shugaban Kasa da majalisun dokoki na kasa da mako daya wato daga 16 ga Fabrairu zuwa 23 ga Fabrairu. Shi kuma zaben gwamnoni da na majalisun dokoki na jihohi aka tura shi zuwa, 9 ga wannan wata.
Kamar yadda na ambata a makalata ta makon jiya, zaben na ranar 23 ga Fabrairu da Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC, ya lashe shi da kuri’a miliyan 15 da dubu 191 da 847, kuma ya samu daga jihohi 19 da kusan dukansu suka fito daga jihohin Arewacin kasar nan, abokin takararsa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zo na biyu da kuri’u miliyam 11 da dubu 262 da 978, wadanda ya samu a jihohi 17 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, kuri’un da akasarinsu suka fito daga jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
Zabubbukan Shugaban Kasar da wakilan majalisun dokoki na kasa zabubbuka ne da za a ce sai sam barka, bisa ga irin yadda gwargwadon zarafi aka yi su cikin kwanciyar hankali da lumana, in ban da ’yan rigingimun da aka samu a Jihar Ribas da aka zargin ’yan sanda sun yi harbi a kan wadanda suka yi niyyar sace akwatin zabe, harbin da ake zargin an yi asarar ran wani mutum. Sai wasu jihohi da aka samu ’yan tashe-tashen hankula da har suka kai ga asarar rayuka da jikkata wadansu. Duk da wadancan tashe-tashen hankula da aka samu za a iya cewa alhamdulillah! Bisa ga irin tashe-tashen hankula da suka rika kai kashe-kashe da jikkata al’umma da aka rika samu tun daga lokacin zabubbukan cikin gida da jam’iyyun kasar nan suka rika gudanarwa tsakanin watan Satumba zuwa farkon watan Oktoban bara da wadanda aka rika yi a cikin gangamin yakin neman zaben da ’yan takarar suka rika gabatarwa.
Mu kanmu ’yan kasa da mutanen kasashen makwabtanmu da masu sa idanu na Nahiyar Afirka da na kasashen duniya, duk mun nuna gamsuwarmu bisa ga abin da muka kira cewa zaben an yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana, sabanin yadda aka yi ta fargabar zai zama tamkar wani yaki. Don haka sakamakonsa ya zama ingantacce gwargwadon zarafi. Mai yiwuwa ganin haka ne ya sa ’yan kasa da kungiyoyi cikin gida da na kasashen duniya suke ta kiraye-kirayen cewa wanda duk bai gamsu da yadda aka gudanar da zabubbukan ba, to, yana da damar ya garzaya zuwa kotun da aka kafa don neman hakkinsa.
Kamar yadda mai karatu ya sani zuwa yanzu sakamakon zabubbukan Shugaban Kasa da na majalisun dokoki na kasa ya faranta wa wadansu magoya baya da ’yan takararsu da suka yi nasara, kamar yadda ya kasance akasi ga magoya baya da ’yan takarsu da ba su yi nasara ba. Alal misali a Jihar Oyo Gwamnan JiharAhaji Abiola Ajimobi na Jam’iyyar APC, ya fadi warwasar a takarar zuwa Majalisar Dattawa da ya nema, haka batun ya kasance a kan takwaransa na Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda ya shiga takarar dan Majalisar Dattawa a inuwar jam’iyyarsu ta PDP, shi da sauran ’yan takara biyu ma sun fadi, ta yadda bayan Shugaba Buhari ya ci jihar ta Gombe, haka sauran ’yan takarar mukaman majalisun dokokin na Jam’iyyar APC suka yi nasara.
A Jihar Sakkwato ma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar (wanda a bara ya bar Jam’iyyar APC ya koma PDP), shi ma jam’iyyarsa ba ta tabuka rawar a-zo-a-gani ba a wancan zabe. Haka labarin ya ke daga Jihar Kwara, inda jagoran tafiyar siyasar da ya gaji mahaifinsa marigayi Dokta Abubakar Saraki a jagorancin mutanen jihar wato Shugaban Majalisar Dattawa mai ci yanzu kuma Darakta Janar na yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar a Jam’iyyar PDP, Sanata Bukola Saraki da ya sake tsayawa takarar Majalisar Dattawa a wancan zabe a jam’iyyarsu ta PDP da ya koma cikinta a bara shi ma da daukacin ’yan takarar Majalisar Dokokin ta kasa labarin ba mai dadin ji ba ne. Don kuwa an kama hanyar kakkabe shi daga harkokin siyasar jihar ta Kwara kwata-kwata.
Abin jira a gani a zaben na gobe idan Allah Ya kai rai shi ne ko a jihohi irin su Kwara da Kano da Jigawa da Sakkwato da makamantansu inda jigororin tafiyar siyasarsu a cikin Jam’iyyar PDP, irin su Sanata Saraki da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano da Alhaji Sule Lamido tsohon Gwamnan Jihar Jigawa da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da iri-irensu da jam’iyyarsu ta PDP da ta sha kashin a wancan zabe ko za su yin wani katabus a zaben na gobe?
Wani abin zuba idanu a gani shi ne irin yadda Hukumar INEC, za ta yi kokarin gyara kura-kuren da aka samu a wancan zabe na ranar 23 ga watan Fabrairu, kamar gaza aikin na’urar tantance masu zabe da aka samu a wasu wurare da batun rashin kai kayayyakin zabe da wuri. Su ma jami’an tsaro musamman ’yan sanda ana fatar su kara kyautata matakan tsaro ta yadda zaben zai fi wanda ya gabace shi tsabta, musamman a kan tsaron doka da oda. Ga ’yan kasa musamman matasa da mata da su ake zargin ’yan siyasa sun fi tunkara wajen ba su cin hanci don su zabe su. Ya kamata irin wadancan masu kada kuri’a su rika karatun ta-natsu, su daina sarayar da ’yancinsu da mutuncinsu da ma na ’ya’yansu a kan ’yan kudi kalilan. An yi zargin cewa har Naira 50, an ba masu kada kuri’a a wasu jihohi, sun zabi wadansu ’yan takara. Ya Ilahi wane irin talauci ne yake damun mutanenmu? A yau me Naira 50 za ta saya koda ga karamin yaro? Ina adduar Allah Ya sa a yi zaben na gobe lami lafiya fiye da ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata, amin summa amin.